✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Jonathan ya yi wa Trump shagube kan faduwa zabe

Tsohon Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ya ce yarda da faduwa a zabe shi ne mafi a’ala don tsira da mutumci. Ana ganin kalaman na Jonathan…

Tsohon Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ya ce yarda da faduwa a zabe shi ne mafi a’ala don tsira da mutumci.

Ana ganin kalaman na Jonathan hannunka mai sanda ne ga shugabanni masu masu fuskantar barazanar shan kaye a zabe, musamman Shugaban Amurka Donald Trump, wanda tun kafin a kirga rabin kuri’un da aka jefa a zabe ya yi ikirarin nasara ya kuma je kotu yana neman ta hana ci gaba da kirga kuri’un.

“Bai dace a zubar da jinin kowa saboda burin wani ba; ka fadi zabi ka tsira da mutuncinka ya fi alheri a kan cin sa bayan kimarka ta zube.

“Ya kamata a kowane lokaci mulki na so da kauna ya rinjayi so ko kaunar mulki.

“Wannan shi ne tsari, kuma ina kwadaitar da shugabanni da ke halin tsaka mai wuya na mulkin gwamnati, zabe ko mu’amalar siyasa da ya rungumi wannan tsari”, inji shi.

Jonathan ya bayyana hakan ne a yayin da ake ci gaba da kirga kuri’un zaben Shugaban Kasar Amurka inda abokin hamayyar Trump kuma tsohon mataimakinsa da suka raba gari, Jeo Biden, ya yi masa fintinkau.

Kokarin Trump na neman a dakatar da kirga kuri’un bayan kallo ya koma sama duba da yadda Biden ke kara ba shi tazara ya ci tura.

Trump ya garzaya kotu yana bukatar a takatar da kirga kuri’un amma alkali ya yi watsi da karar, lamarin da ya ja ake ta zolayarsa yayin da Biden ke kara samun rinjaye.

Ana dai ganin kalaman na Jonathan shagube ne ga Trump duk da cewa tsohon shugaban na Najeriya bai kama suna ba.

A mako mai zuwa ake sa ran sanar da sakamakon zaben wanda aka fara ranar 2 ga Nuwamba, 2020.

Idan Biden ya yi nasara, to Trump zai shiga sahun shugabannin Amurka da hakarsu ba ta cimma ruwa na yin tazarce ba, Biden kuma zai shiga jerin shugabannin kasar mafiya yawan shekaru a laokacin da suka dare kan mulki a fadar White House.

Idan kuma Trump ya koma, to zai shiga jerin shugabannin da zaben tazarcensu ke cike da rudani suka kuma sha da kyar.

A yayin da ake dakon sakamakon a hukumance, ana zaman dar-dar game da abin da ke iya faruwa.

A 2015 Jonathan ya sha kayi bayan da ya nemi tazarce a karkashin inuwar jam’iyar PDP inda shugaba mai ci a yanzu, Muhammadu Buhari ya samu nasara a kansa.

Bayan Buhari ya yi masa fintinkau, tun kafin a kammala kirga kuri’un zaben a hukumance Jonathan ya rungumi kaddara ya kira Buhari ya taya shi murna.

%d bloggers like this: