An shiga ruɗani a wannan Talatar yayin da mutane suka kasa shiga shafukansu na Facebook da Instagram.
Masu amfani da shafukan Facebook da Instagram sun shiga ruɗani bayan da Kamfanin Meta — mamallakin shafukan sada zumuntar — ya gamu da tangarda a Yammacin ranar Talata.
Dubban ma’abota shafukan ne suka fara bayyana koke a yanar gizo yayin da masu amfani da Facebook, Messenger, da Instagram suka ruwaito cewa an kore su daga shafukansu ba tare da sanarwa ba.
Wannan lamari na gama-gari ya fara nunawa akan na’urorin mutane a Amurka, daga bisani kuma ya karade kusan ko’ina a faɗin duniya.
Da yawa daga waɗanda suka yi yunkurin shiga shafukansu sun farga da tangardar, lamarin da ya janyo cece-ku-ce a intanet.
Da farko dai dubban masu amfani ne suka fara fuskantar matsalar, amma daga bisani cikin kankanin lokaci ta koma miliyoyi.
Har ya zuwa yanzu ba a samu tabbacin dalilin afkuwar wannan lamari ba.