Daga hudubar Yaseen Bi’asba’i
Masallaci: Ba a fada ba
Fassarar Salihu Makera
Huduba ta farko
Hamdala da taslimi. Bayan haka, ya ku bayin Allah! Lallai mumini zai rika ganin juyi a wannan zamani idan Allah Ya tsawaita rayuwarsa, ta yadda a kowace rana zai rika samun ganimar da zai yi guzurin Lahira da ita. Allah Madaukaki Ya ce: “Kuma Shi ne Wanda Ya sanya dare da yini a kan mayewa, ga wanda yake son ya yi tunani, ko kuwa ya yi nufin ya gode.” (K: 25:62).
Ya ku muminai! Mai rabo, ya samu rabo a watan Rajab, ta wajen ayyukan da’a da kusanci ga Allah. To ga shi mun shigo watan Sha’aban, me muka shirya yi a cikinsa?
An kira wannan wata Sha’aban ne saboda Larabawa suna watsuwa a cikinsa don neman ruwa. Wadansu kuma sun ce, ana kiransa da Sha’aban ne saboda watsuwarsu wajen kai hare-haren yaki bayan fita daga watan Rajab Mai alfarma da aka hana yaki a cikinsa. Amma wadansu sun ce saboda wata ne da ke bayyana, a tsakanin Rajab da Ramadan.
Dangane da falalarsa da abin da ake son a yi a cikinsa, hakika ya zo daga Ahmad da wadansu, kuma Ibn Khuzaima ya inganta shi, sannan Albani ya kyautata shi daga Usama bn Zaid (RA), ya ce: “Na ce: “Ya Manzon Allah! Ban gan ka kana azumtar wani wata kamar yadda kake azumtar Sha’aban ba! Sai ya ce: “Wannan wata ne da mutane suke gafala daga gare shi a tsakanin Rajab da Ramadan. Shi ne watan da ake daukaka ayyuka zuwa ga Ubangijin talikai. Don haka nake son a daukaka aikina ina cikin azumi.”
Ya ku Musulmi! Ba ku ganin yadda mutane suke gafala daga watan Sha’aban? Suna gafala daga ayyukan da’a da kusanta ga Allah. Suna nutso a cikin sha’awoyi da ayyukan jin dadi. Suna gafala daga Sha’aban alhali Manzon Allah (SAW) ya kasance yana raya shi da ayyukan da’a da azumi. Ku tuna ya ce wa Usama: “Wannan wata ne da mutane suke gafala daga gare shi a tsakanin Rajab da Ramadan.”
Mutane suna gafala daga Sha’aban saboda yana tsakanin watanni biyu masu girma wato Rajab Mai alfarma da Ramadan Mai albarka. Mutane sun fi shagala da watanni biyun, don haka sai aka shagaltar da su daga gare shi. Ta kai wadansu mutane suna ganin azumin watan Rajab (azumin tsofi in ji Hausawa), ya fi azumin Sha’aban, saboda shi Rajab wata ne Mai alfarma. Wannan ba daidai ba ne, azumin Sha’aban ya fi na Rajab falala saboda fadin Annabi (SAW): “Ana daukaka ayyukan a cikinsa, kuma ina son a daukaka aikina ina azumi.”
Hakika malamai (Allah Ya yi musu rahama) sun ce: “A cikin wannan Hadisi akwai dalili na cewa mustahabbi ne a raya lokutan da mutane suka gafala da ayyukan da’a, kuma hakan abin so ne a wurin Allah Mabuwayi.”
Don haka ku koma ga Allah ya ku bayin Allah! Ku sallama ga abin da Yake yarda da shi, domin lada da ijara suna kara martaba idan aka yi su a lokacin da mutane suka gafala, fa’idojin raya shi da da’a su ne mafiya girma. Kuma wadannan fa’idoji za a same su ne idan aka yi ayyukan da’ar a asirce tare da boyewa. Sirrantawa da aikata aikin da’a a boye daya ne daga cikin manya sabubban karbar aiki. Akwai bukatar aiki ya kasance don Allah, a nesanta shi daga jiyarwa da riya.
Ku sani aikin da’a a lokacin gafalar mutane yana da wahala a tsakanin mutane. Mafiya falalan ayyuka, su ne wadanda suka fi wahala ga mutane matukar suka dace da Sunnar Annabi (SAW). Manzon Allah (SAW) ya ce: “Ladar aiki na dogara ne da irin wahalar da aka sha a kai.”
Ya bayin Allah! Lallai ana daukaka ayyukan shekara zuwa ga Allah a watan Sha’aban. Ayyukan bayi suna bijirowa ga Allah bijirowa a kowane wuni da dare, sannan ayyukan mako su bijiro gare Shi a kowace Litinin da Alhamis, sannan a bijiro da ayyukan shekara a Sha’aban. Ga kowace bijirowa akwai hikima, Allah Yana bayyana su ga wanda Ya so daga cikin halittunSa, ko Ya asirta su a wurinSa, alhali babu abin da Yake boyuwa ga Allah daga ayyukan bayinSa.
Ya ku muminai! A yayin da Sha’aban ya zama kamar kofar shiga Ramadan – kuma ba makawa hakan ne – sai aka shar’anta yin azumi da sauran ayyukan da’a a cikin watan Sha’aban domin kusantar Allah ta yadda za a yi tattalin zuwan Ramadan, a tarbe shi cikin annashuwa da shauki da sabawa da da’a ga Mai rahama. Don haka ne Annabi (SAW) yake yawaita azumi a cikinsa, yake cin ganimar lokacin gafalar mutane duk da matsayinsa, na wanda aka gafarta masa abin da ya gabatar da wanda ya jinkintar na zunubinsa. Don haka ne magabatan kwarai suke kara kokari a cikin watan Sha’aban suke tattalin zuwan Ramadan wajen yin ayyukan da’a.
Ya kai bawan Allah! Me ka shirya a Sha’aban don marabtar Ramadan? Wane tattali ka yi masa?
Ka yi tattalin kanka da abin da Manzon Allah (SAW) ya kwadaitar, wato yawaita azumi a watan. Hakika Annabi (SAW) yana yawaita azumi a cikinsa. An karbo daga A’isha (Allah Ya yarda da ita da mahaifinta) ta ce: “Manzon Allah (SAW) ya kasance yana azumi har sai mun ce ba ya sha ruwa, kuma yana shan ruwa har sai mun ce ba ya azumi (a sauran watannin shekara). Amma ban taba ganin Manzon Allah (SAW) ya yi azumin wata guda ba, sai Ramadan. Kuma ban taba ganin ya yawaita azumi a wani wata fiye da Sha’aban ba.” Buhari da Muslim suka ruwaito.
A wata ruwaya ta Buhari ya ce, “Ya kasance yana azumtar Sha’aban dukansa.” Muslim kuma ya ruwaito cewa: “Yana azumtar Sha’aban sai dan kadan.” A ruwayar Abu Dawud ta ce: “Watan da Manzon Allah (SAW) ya fi son ya azumta shi ne Sha’aban, sannan ya sadar da shi da Ramadan.”
Dukan wadannan Hadisai ingantattu ne, kuma wannan yana nuni ne da tsananin kiyayewarsa ga azumi a cikin Sha’aban. Manufa ita ce ya fi yin azumi a cikinsa ba wai yana azumtarsa gaba daya ba ne.
Ibn Hajrin (Allah Ya yi masa rahama) ya ce: “Ya fi yin azumin tadawwa’i a cikin Sha’aban fiye da kowane wata. Ya kasance yana azumtar mafi yawan kwanakin Sha’aban.”
Ya ku Musulmi! Malamai sun ce: “Yin azumi a Sha’aban ya fi falala daga yin azumi a sauran watanni kamar azumin Muharram, wanda shi ne mafi falalar azumi a bayan Ramadan. Domin falalar azumin tadawwa’in (na Sha’aban) ya kasance a kusa da azumin farilla na Ramadan a gabansa ko bayansa. Domin yana daf da azumin Ramadan sai ya yi kamar an jeranta azumin sunnoni da na farilla a gabansa da bayansa. Don haka azumin Sha’aban kamar Sunnah ce ta kabliyya ga Ramadan, yayin da azumin shida na Shawwal suke zaman Ba’adiyya gare shi. Jerantattun kuwa sunnoni sun fi tadawwa’in da ke zaman kansa cikin abin da ya shafi Sallah. To kamar haka lamarin yake, cewa yin azumi a gabani ko bayan Ramadan ya fi falala daga yin azumi mai zaman kansa da bai saduwa da shi.
Ibn Rajab (Allah Ya yi masa rahama) ya ce: “Game da azumin Sha’aban an ce: “Azumtarsa kamar jarrabawar share fage ce ga shiga azumin Ramadan, domin kada mutum ya shiga azumin Ramadan bisa wahala. Kai yakan zamo mutum ya san wani abu kan azumin tare da sabawa da shi, ya samu dandanon Ramadan ta hanyar azumin Sha’aban, kuma ya shiga watan azumin Ramadan da karfin jiki da nishadi.”
Ya bayin Allah! Wanda azumin Sha’aban zai raunana shi daga yin azumin Ramadan, to, ya dakatar da azumin idan Sha’aban ya je kusan karshe, saboda fadinsa (SAW): “Idan Sha’aban ya kai karshe, kada ku yi azumi har zuwa Ramadan.” Ahmad da wadansu suka ruwaito, Albani ya inganta shi, amma a isnadinsa akwai magana.
Hanin da ke cikin Hadisin domin a samu karfin yin azumin Ramadan ne. Wadansu sun ce: “Hanin a kan wanda ya sha ruwa ne, bai azumci farkon watan ba, don haka idan Sha’aban ya zama saura kadan ba zai yi azumin ba.
Na biyu: Ya kai bawan Allah! Da me za ka kintsa kanka domin shiga Ramadan? Ka kintsa kanka da abin da ya sawwaka na aikin da’a, kamar yawaita karatun Alkur’ani da sadar da zumunta da sauransu. Salmata bn Kuhail ya ce: “Ana cewa: “Watan Sha’aban watan masu karatu.” Abubakar Albalkhiy kuma ya ce: “Watan Rajab watan shuka, watan Sha’aban watan ban-ruwa, watan Ramadan kuma watan girbi. Wanda bai yi shuka a Rajab ba, bai bayar da ruwa a Sha’aban ba, ta yaya zai yi girbi a Ramadan?”