✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sergio Ramos ya bar kungiyar Real Madrid

Dan wasan ya shafe shekara 16 yana murza leda a kungiyar Real Madrid.

Ta tabbata dan wasan bayan Real Madrid kuma kaftin dinta, Sergio Ramos ya bar kungiyar bayan shafe shekara 16.

Rahotanni daga kasar Spain sun ce Ramos zai tattauna da manema labarai a ranar Alhamis don tabbatar musu da barin kungiyar, bayan shafe tsawon lokaci ana tattauna game da makomarsa.

  1. Zamfara: An kashe ’yan bindiga da dama yayin artabu
  2. Ronaldo ya ja wa Coca-Cola asarar Dala biliyan 4

Dan wasan mai shekara 35 ya buga wasanni 21 a bana, inda ya zura kwallaye hudu tare da taimakawa wajen zura guda daya.

Ramos ya sha fama da rauni a kakar wasan da aka kammala a bana, wanda hakan ya sa bai samu damar shiga ciki jerin ’yan wasan da za su wakilci Spain a gasar Euro 2020 ba.

An jima ana rade-raden zai iya komawa kungiyar PSG, Manchester City ko kuma Sevilla.