A ranar Litinin ce Kwamitin Shirya Gasar Olamfik ya sanar da kasar Senegal a matsayin wadda za ta dauki nauyin gasar Olamfik na matasa a shekarar 2022.
Babban Darakta a Kwamitin shirya gasar Olamfik ta duniya Christophe Dubi ne ya sanar da menama labarai haka. Ya ce wannan ne karon farko da wata kasa daga Nahiyar Afirka za ta dauki nauyin gasar Olamfik. Ya ce an zabi Senegal ce bayan ta doke wasu kasashe uku da suka fafata a kokarin daukar nauyin gasar.
Shugaban Kasar Senegal Macky Sall ya bayyana farin cikinsa game da wannan dama da aka ba kasarsa ta daukar nauyin gasar.
Ya ce ana sa ran kasarsa za ta kashe kimanin Dala miliyan 150 (kimanin Naira biliyan 129) wajen gina sababbin filayen wasanni kafin a fasar gasar ta Olamfik.
Ya ce za a gina filayen wasanni ne a biranen Dakar da Diamniadio da kuma Saly da za su rika cin ’yan kallo dubu 50 kowannensu.
Mataimakin Shugaban Kwamitin Shirya Gasar Olamfik, Mista Ugur Erdener ya ce ana sa ran za a gudanar da gasar Olamfik ta matasa ce a Senegal a watan Mayun 2022 lokacin da aka fita daga yanayin zafi.
Gasar Olamfik ta kunshi wasanni daban-daban da suka hada da guje-guje da tsalle-tsalle da kwallon tebur da na tenis da kwallon kwando da ninkaya da kwallon kafa bangaren maza da mata da jifar mashi da sauransu. Ana sa ran fiye da kasashe 100 daga sassan duniya ne za su halarci gasar.
A 1996 ne Najeriya ta zama zakara bayan ta lashe lambar zinare a gasar kwallon kafa ta maza a wasan.