Fitaccen mai zanen barkwanci, Mustapha Bulama ya ce sun hango irin matsalar da ta samu masu zanga-zangar #EndSARS tun wuri ne, shi ya sa suka dakatar da zanga-zangar a kawo zaman lafiya a Arewa ta #SecureNorth.
Bulama, wanda shi ne Kakakin #SecureNorth ya bayyana hakan ne a zantawarsa da Aminiya, inda ya ce su ma masu kawo tarzoma sun fara rabar su kafin suka farga.
“Dama mun yi zanga-zangar #SecureNorth ce domin mu jawo hankalin gwamnati a kan kashe-kashe da ake yi Arewacin Nijeriya.
“Burinmu shi ne mu isar da sako ga gwamnati musamman shi Shugaban Kasa Muhammdu Buhari a kan a ba Arewa tsaro.
“To bayan mun fara, mun yi kwana uku, sai muka fahimci akwai wasu mutane da suka zo suna so su jawo tarzoma.
“Sai muka ga cewa tunda muna yi ne a kan samar da tsaro a Arewa, yankin da dama ke fama da rashin tsaro, bai kamata mu yi abin da zai rikide ya zama tarzoma da zai kara wa yankin rashin tsaro ba.
“Da muka fahimci haka, sai muka ce mun janye muka kuma fitar da sanarwar cewa mun janye zanga-zangar a tituna, za mu dawo a kafafen sadarwa mu ci gaba da bayyana bukatunmu.
“Wannan wani dogon tunani ne da muka yi wanda masu zanga-zangar #EndSARS ba su yi ba, wadanda duk da cewa an amince musu da bukatunsu, amma suka ki daina zanga-zangar, har abin da muke tsoro ya same su — wasu suka shiga cikinsu suka jawo tarzoma, aka yi rikice-rikice har aka yi asara”, inji Mustapha Bulama.
Da Aminiya ta tambaye shi ko za su ci gaba da zanga-zangar ta #SecureNorth bayan an samu kwanciyar hankali daga yamutsin da zanga-zangar #EndSARS ta jawo, sai ya ce, “Za mu ci gaba da zanga-zangar amma ta wasu hanyoyi, ba dole sai mun tara mutane a tituna ba.
“Za mu dubi duk wata hanya da ta dace da ba za ta kawo rashin tsaro ba domin mu isar da sakonmu a kan a samu zaman lafiya a Arewa”, inji shi.
Daga fitattun mutanen da suka shiga zanga-zangar ta #SecureNorth akwai manyan jaruman masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood irinsu Ali Nuhu da Aminu Saira da Ali Jita da Fresh Emir da sauransu.