Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Human Rights Watch ta ce yadda Saudiyya ke fitar da makudan kudade wajen sayen fitattun ’yan wasan kwallon kafa na dauke hankalin duniya daga laifukan da kasar take aikatawa.
Wannan na zuwa ne a yayin da Human Rights Watch ta ce Saudiyya na gallaza wa ’yan ci-rani daidai lokacin da kasar ke kokarin gyara mutuncinta a duniya.
- ’Yan ta’adda sama da 100 sun mutu a gumurzu tsakanin Boko Haram da ISWAP
- ’Yan sanda sun haramta zanga-zanga a Kano
Cikin sanarwar da ta fitar, Nadia Hardman, wata jami’ar kungiyar ta Human Rights Watch, ta ce bai kamata kudaden da Saudiyya ke kashewa wajen sayen fitattun ’yan wasan kwallon kafa na duniya su dauke hankulan mutane daga wadannan laifuka masu muni da hukumomin Saudiyya ke yi wa dan Adam ba.
Human Rights Watch ta ce jami’an tsaron kan iyaka na Saudiyya sun harba makamai masu hatsari ga wasu ’yan ci-rani da ke hankoron shiga kasar ta mashigar kasar Yemen.
Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Human Rights Watch ce ta yi zargin hakan a wannan Litinin.
Kungiyar ta ce wannan cin zali na jami’an na Saudiyya tuni ya yi ajalin daruruwan ’yan ci-ranin da galibinsu suka fito daga kasar Habasha.
Kawo yanzu hukumomin Saudiyya ba su kai ga mayar da martani ga wannan zargi ba.