✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwankwaso ne ya fara sayar da kadarorin Gwamnatin Kano —Ganduje

Idan mutum yana ja, ya je gidan rediyo ...idan lissafin wadanda suka amfana za a yi, to sai an kwana ba a gama ba

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya yi wankin babban bargo ga masu zargin gwamnatinsa da cefanar da kadarorin gwamnatin jihar, inda ya ce ba a kansa aka fara ba.

Ganduje, wanda gwamnatinsa ta yi kaurin suna wajen sayar da wasu kadarorin jihar ya ce kafin shi, Gwamna Kwankwaso da ya yi maitamaki a baya ma, ta sayar da su.

“Idan mutum yana ja, ya je gidan rediyo za mu gaya, wanda kuma na tabbatar idan lissafin wadanda suka amfana za mu yi, to sai mu kwana ba mu gama ba,” in ji shi.

Gwamnan ya yi wannan martani ne a lokacin da ya jagorancin bude sabon ginin Ma’aikatar Matasa da Wasanni ta jihar wanda gwamnatinsa ta samar.

Kalaman nasa na zuwa ne bayan kwamitin karbar mulki na gwamnatin jihar mai jiran gado ta Jam’iyyar NNPP, wadda Kwankwaso ke jagoranta, ke cewa sabuwar gwamantin za ta kwace kadarorin da gwamnatinsa ta sayar.

Ko a makon jiya, sai da kwamitin ya zargi Ganduje da yi wa dansa gwanjon wani katafaren ginin gwamnati a kan kudin da ba su taka kara ya karya ba, tare da alkawarin sabuwar gwamnati za ta kwace shi, bayan ta karbi ragamar mulkin jihar.

Amma a martanin Ganduje, ya ce, “Wannan abin ba wai daga gwamnatin jihar aka fara ba, har Gwamnatin Tarayya ma tana sayar da kadarorinta, domin ni na yi aiki a Gwamnatin Tarayya an ba ni gidan gwamnati amma daga baya an sayar min da shi.”

Ya ci gaba da cewa, “Sai ga wani mutum mai baki da kunu, kafarsa da kirci, kansa da kora yana ihu cewa wai mun sayar da kadarorin gwamnati to muna gaya masa ya je ya tambayi ubansa ko kakansa a siyasa domin shi ya fara yi.

“A wancan lokacin mun sayar wa da ma’aikata da yan siyasa da sauran mutane.

“Idan mutum yana ja, ya je gidan rediyo za mu gaya, wanda kuma na tabbatar idan lissafin wadanda suka amfana za mu yi to sai mu kwana ba mu gama ba.”

Gwamnan ya ce tuni gwamnati ta daina gina gidaje ta sa ma’aikata a ciki sai dai ta sayar da su.