Sufeto-Janar na ’Yan Sandan Najeriya, Usman Alkali Baba, ya ce suna gudanar da bincike kan wasu gwamnoni da ke furta kalaman tunzuri da suka haddasa tarzoma kan dokar canjin kudi a Najeriya.
Baba ya bayyana hakan ne a ganawarsa da ’yan jarida a Abuja, bayan taron Majalisar Zartaswa ta Kasa da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta.
- Samamen DSS a ofishin NNPP ya bar baya da kura a Kano
- Kotu ta daure ’yan jaridar bogi a gidan yari a Kano
Ya ce duk da doka ba ta ba su damar kama gwamnan da ke kan mulki ba saboda kariyar da ta ba shi, babu shakka za su gurfanar da duk wanda bincikensu ya nuna ya aikata laifin a gaban kotu.
“Dukkanmu mun san dalilin da ya sa gwamnonin ke yin hakan, amma mun fara gudanar da bincke.
“Watakila sun dogara da kariyar da doka ta ba su, amma wannan ba zai hana mu gargade su da kuma ba su shawara ba, kamar yadda muke yi a yanzu”, in ji shi.
Baba ya ce tuni ’yan sanda suka samu nasarar kwantar da tarzomar, tare da tabbatar wa ’yan Najeriya cewa babu wata matsalar tsaro da za ta biyo baya a lokacin zabe.