✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sauye-sauyen da Tinubu ya yi wa fannin tsaro a kwana 100

Tsaro ne zai zama babban ƙudirin wannan gwamnatin.

A ranar 29 ga watan Mayun 2023 ne aka rantsar Bola Ahmed Tinubu a matsayin Shugaban Najeriya dandalin Eagles Square da ke Abuja bayan karewar wa’adin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.

A yayin taron wanda shugabannin ƙasashen duniya kimanin 24 suka halarta, jawabin da Tinubu ya gudanar cike yake da ƙarfafa gwiwar ’yan Najeriya, da neman haɗin kan ƙasa.

Daga cikin muhimman alƙawuran da ya ɗauka, Tinubu ya ce magance matsalar tsaro zai saka a gaba tsawon shekara huɗu masu zuwa.

A cewarsa “Tsaro ne zai zama babban ƙudirin wannan gwamnatin, saboda ba za a samu adalci ba ko cigaba matuƙar akwai rashin tsaro da tashin hankali.

“Don daƙile wannan bala’i, dole ne mu gyara tsarin tsaronmu da ma fasalinsa. Za mu ware ƙarin kuɗi ga jami’an tsaronmu, ba wai yawansu kawai za mu ƙara ba.

“Za mu ba su ƙarin horo, da kayan aiki, da ƙarin albashi, da kuma makamai,” kamar yadda ya bayyana.

Nadin ‘NSA’

A ranar 15 ga watan Yuni ne Tinubun ya naɗa masu ba shi shawara kan harkoki daban-daban ciki har da tsohon shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (EFCC), Mallam Nuhu Ribaɗu a matsayin mai ba shi shawara kan harkokin tsaro na musamman.

Sai dai kuma, a ranar 19 ga watan Yuni ne ya daga likafar Nuhu Ribaɗu zuwa Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara kan tsaron kasa National Security Adviser (NSA), kamar yadda wata sanarwa da Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya ta tabbatar.

Sallamar manyan hafsoshin tsaro

A wannan rana ce kuma Tinubun ya amince da naɗa sabbin manyan hafsoshin tsaron Najeriya da kwamandojin fadar shugaban ƙasa.

Matakin na zuwa ne bayan sabon shugaban ya sanar da matakin sallamar hafsoshin da ke jagorantar rundunonin tsaron ƙasar daga aiki nan take.

Tinubun dai ya naɗa Manjo Janar C.G Musa a matsayin Babban Hafsan Soji, bayan sallamar Laftanar-Janar Lucky Irabor.

Sai Manjo Janar T. A Lagbaja a matsayin Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya, inda ya canji Laftanar-Janar Faruk Yahaya.

Haka zalika, Riya Admiral E. A Ogalla ya zama Babban Hafsan Sojin Ruwa na Najeriya, inda ya maye gurbin Vice Admiral Awwal Zubairu Gambo.

Akwai kuma Air Vice Marshal H.B Abubakar a matsayin sabon Babban Hafsan Sojin Sama, inda ya gaji Air Marshal Oladayo Amao.

Sabbin shugabannin hukumomin tsaro

Ƙarin manyan jami’an tsaron har da DIG Kayode Egbetokun a matsayin Babban Sufeton ’Yan Sandan Najeriya, inda ya maye gurbin Usman Alƙali Baba.

Haka kuma sanarwar ta ce Shugaba Tinubu ya naɗa Manjo Janar EPA Undiandeye a muƙamin Babban Hafsan Tattara Bayanan Sirri na Tsaro wato Defence Iintelligence.

Bugu da ƙari, Shugaban ya amince da naɗin waɗannan jami’ai:

  • Kanar Adebisi Onasanya – Kwamandan Rundunar Tsaron Shugaban Kasa
  • Laftanar-Kanar Moshood Abiodun Yusuf, Kwamandan 7 Guards Battalion, Asokoro, Abuja
  • Laftanar-Kanar Auwalu Baba Inuwa 177, Guards Battalion, Keffi, Jihar Nasarawa.
  • Laftanar-Kanar Mohammed J. Abdulkarim 102 Guards Battalion, Suleja, Jihar Neja.
  • Laftanar-Kanar Olumide A. Akingbesote 176 Guards Battalion, Gwagwalada, Abuja

Jami’a Fadar Shugaban Kasa:

Sai kuma jami’an Fadar Shugaban Ƙasa da naɗin ya shafa:

  • Manjo Isa Farouk Audu – Kwamandan Rundunar Atilare ta Fadar Shugaban Kasa
  • Kaftin Kazeem Olalekan Sunmonu – Mataimakin Kwamandan Rundunar Atilare ta Fadar Shugaban Kasa
  • Majnjo Kamaru Koyejo Hamzat – Kwamandan Rundunar Tara  Bayanai ta Fadar Shguaban Kasa
  • Manjo TS Adeola – Kwamandan Rumbum Makamai na Fadar Shugaban Kasa
  • Laftanar A. Aminu – Mataimakin Kwamandan Rumbum Makamai na Fadar Shugaban Kasa
  • A ƙarshe, Tinubu ya amince da naɗin Adeniyi Bashir Adewale a matsayin Muƙaddashin Kwanturola-Janar na Hukumar Kwastam.