Kungiyar Tuntuba ta Arewa, (ACF) ta ce sauya tsarin Najeriya abu ne da yiwuwarsa ke da wuya duk da yawaitar kiraye-kirayen yin hakan a kasar.
Shugaban ACF, Audu Ogbeh, ya bayyana cewa da wuya Najeriya ta koma tsarin mulkin yankuna inda kowane yanki ke da ikon gudanar da albarkatunsa.
- An yanke wa matashi hukuncin daurin rai-da-rai saboda yi wa agolarsa fyade
- Shugaban makaranta yi wa karamar yarinya ciki a Katsina
- Ta yi garkuwa da saurayi saboda ya ki auren ta
- An cafke jami’in tsaron ABU da ke hada baki ana garkuwa da mutane
“Sauya tsairin kasa abu ne mai muhimmanci domin magance matsalolin kasar nan. Amma abin tambaya shi ne ta wace hanya za a yi?
“Shin jihohi za su sarayar da ikonsu ne? Da kamar wuya. Za a koma tsarin yankunan siyasa kamar 1960 ne? Shi ma da kyar zai yiwu. A nan matsalar take,” inji Audu Ogbeh.
Ya bayyana haka ne a taron Tattaunawar Daily Trust karo na 18, wanda ya tattauna kan sauya tsarin Najeriya, batun da aka jima ana muhawar a kai a kasar.
Audu Ogbeh, wanda tsohon Ministan Noma ne ya koka game da mutuwar manyan masana’antu a fadin Najeriya, inda ya ce a Kano kadai masana’antu 126 ne suka mutu a cikin ’yan shekaru.
“Tattalin arzikin kasar nan na saurin mutuwa kuma wannan hadari ne a nan gaba domin ta nan ne al’ummomi da ke tasowa za su fahimci ba su abin da rayuwarsu za ta dogara da shi a gaba.
“Babbar matsalar ita ce ta tattalin arzikin kasar nan. A cikinmu mutum wa zai iya kirga yawan masana’antun da suka mutu? Daga yankin Kudu maso Yamma, Arewa da kuma Gabas.
“A Kano kadai, masana’antu 126 sun durkushe. Ana maganar samar da ayyukan yi amma ko rance ba za ka iya samu daga banki ba. Kudin ruwan kashi 5% kadai. Ko hodar ibilis kake sayarwa ba za ka kai labari ba,” inji shi.