Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Ina mana marhabin da sake haduwa cikin wannan fili. Da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin.
Na ji dadin bayaninku kan yaren kauna, ya warware mini wani abu da ya shige mini duhu game da maigidana; domin duk wani abin burgewa da jan ra’ayin maigida da na ji ko na karanta sai na jarraba gare shi, amma ba na ganin wani canji kuma ba ya nuna mini jin dadinsa. Yanzu na fahimci kila ba da yaren da zai fahimta nake masa ba shi ya sa. Tambayata ita ce ya zan yi in fahimci yaren kaunarsa kuma ya zan yi in fahimtar da shi nawa yaren kaunar?
—Maman Ihsan, Katsina.
Amsa
Kamar yadda ya zo a makon da ya gabata, yaren kaunar ma’aurata guda hudu ne: Kalaman kauna; Kyauta da kyautatawa; Shafar kauna da kuma Ayyukan sadaukarwa; ga bayani kan siffofinsu da kuma yadda ake aikatar da su cikin rayuwar aure. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma ya amfanar da su, amin.
1. Kalaman kauna: Wannan yare yana da matukar muhimmanci da tasiri sama da sauran yaruka ukun, domin kowannensu yana bukatar wani kaso daga cikin kalami; kuma saboda kaifin tasirin magana, nan da nan take gyarawa kuma nan da nan take batawa. Ga wanda yaren kaunarsa ya kasance yawan jin kalamai da kalmomin bayyana kauna ne, zai kasance kullum cikin jin yunwa da kishirwar sauraren wadannan kalmomin daga wajen abokin aurensa, domin suna dadada masa rai, su tsundumar da shi cikin tsananin farin ciki da natsuwar rai. Haka nan kalamai marasa dadi, na kushewa, jin haushi da na tsana suna tsundumar da shi cikin bakin ciki marar misaltuwa kuma ya kan dade bai manta da su ba.
Sautukan Kalami:
1. Kalaman Bayyana Shaukin So: Masu irin wannan yaren ba sa gajiya da jin kalmomin kauna kamar su: Ina tsananin sonka/ki; kallon murumushinki yana shagaltar da ni; ba zan daina sonki ba har abada; da sauransu. Don haka sai ma’aurata su rika yawan fada wa junansu, ko a wakoki suka ji wasu kalaman kauna sai su rike su, sannan su daidaici lokacin mafi dacewa sannan sai su fade su ga masoyinsu cikin siga mafi dacewa.
2. Kalaman daukakawa: Su ne kalaman yabo, kirari kambamawa, kodawa da jinjinawa. Maigidan da yaren kaunarsa ya kasance jin kalaman kauna ne, to kullum in ya shirya zai tafi wajen aiki, ko in ya yi wankan yamma zai fita, ya kamata Uwargida ta koda shigar da ya yi, kayan da ya sa da sauran wani abin burgewa da suka bayyana gare ta daidai da lokaci da kuma yanayi. Haka kuma kamar lokacin da Maigida ya dawo, Uwargida ta tare shi da murna ta yi masa sannu da zuwa, to wannan bai isa ga maigidan da kalami shi ne yaren kaunarsa ba, dole sai ta hada da wasu kalmomin kamar ta ce: “Wai! Har na ji wata ni’ima ta sauka cikin gidan nan, rai na ya yi fari kal da dawowarka maigida!” Ko wani kalami makamancin haka, to wannan zai sa ya ji dadi, kila ma ko da ya yi niyyar fita yana iya fasawa, saboda da wannan kalamin. Haka ma ga uwargidan da yaren kaunarta ya kasance kalami ne, yaba kwalliyyarta da cewa “kin yi kyawu kadai,” ba ya isa sai an hada da wasu kalaman kodawa kamar a ce “Ni sai na ga kin koma kamar wata sabuwar budurwa Wallahi! Wannan irin kyau! Har yana sa numfashina na daukewa!”
Kalaman yabo da kodawa ba dole sai an ga wani abun burgewa za a fade su ba: Ba dole sai uwargida ta caba ado ne kadai za a yaba kyawunta ba, ko tana cikin aikin gida, ba a ado a tare da ita, maigida na iya koda ta dai: Kai! Ni uwargida komai naki daban ne, daurin gaban ma sai kin yi yadda za ki shagaltar da mutum da shi,” ko wata daddadar magana.
Haka kuma maza suna son koda girmansu, darajarsu da iyawarsu, don haka uwargida sai ta rika yawan koda maigidanta da yi masa kirari da kambamawa. Ita kuma uwargida tana jin dadin a yaba yammakantakarta, yaranta da girkinta.
3. Kalaman goyon baya da karfafa gwiwa: Irin wadannan kalamai lokacin da yanayin zamantakewa ke kawo su, don haka sai a kiyaye, don bayyanar da irin wannan kalaman lokacin da ake bukatarsu, kamar lokacin da ake fuskantar wani muhimmin burin rayuwa, mutum na bukatar kalaman karfafa gwiwa a irin wannan lokacin.
Sai sati na gaba in sha Allah. Da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarsa a kodayaushe, amin.
Sautukan Yaren kauna
Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Ina mana marhabin da sake haduwa cikin wannan fili. Da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da…