Wani saurayi ɗan shekara 24 ya shiga hannu kan zargin jefa wata budurwa ’yar shekara 17 a rijiya bayan ya yi mata fyaɗe a Jihar Katsina.
Matashin ya yi wa yarinyar wannan aika-aika ne bayan ya yi arba da ita a lokacin da mahaifiyar ta aike ta a Rukunin Gidajen Jakadu da ke garin Katsina.
Rundunar ’yan sandan jihar ta ce wanda ake zargin ya yi wa yarinyar barazana ne da wata sharɓeviyar wuka, inda ya tisa ƙeyarta zuwa wani kango ya keta huruminta da ƙarfin tsiya.
Bayan ya kammala kuma a ƙoƙarinsa na ɓatar da sahun abin da ya aikata ne ya jefa ta a cikin wata rijiya sannan ya jefa duwatsu a ciki a a ranar 27 ga watan Satumba.
- Jikan Sarkin Zazzau Shehu Idris Ya Zama Sabon Dan Isan Zazzau
- Tubabbun ’yan Boko Haram da ke taimaka wa sojoji sun tsere da makamansu
Duk da haka, Allah Ya yi mata gyaɗar dogo, inda daga bisani ’yan sanda suka ceto ta taga rijiyar, bayan gudanar da bincike kuma suka cika hannu da wanda ake zargin.