Rundunar ’Yan Sanda na musamman mai yaki da ’yan bindiga da ’yan ta’adda, wato IRT wadda, ta bajekolin wani saurayi da wata budurwa da suke safarar ’yan mata zuwa dabar ’yan bindiga da ke Dajin Galadimawa a Zariyan Jihar Kduna.
Babban Sufeton ’Yan Sanda na Kasa ne dai ya kafa rundunar don yaki da ’yan ta’addan.
- Miji ya dauki hayar abokinsa a N10,000 don ya kashe matarsa mai juna biyu
- Dole a yi watsi da manyan jam’iyyu, inji Bashir Tofa a hirarsa ta karshe
Rundunar, ta ta samu nasarar kama saurayin da budurwar da suke aikin safaran ’yan matan domin su kai wa ’yan bindigar don yin lalata da su..
Saurayin dai dan asalin anguwar Sakadadi ne kuma yana sana’ar sayar da wayar hannu a kasuwar ’yan waya da ke PZ a Sabon Garin Zariya ta Jihar Kaduna.
Ita kuwa budurwar, abokiyar aikinsa ce mai kimanin shekara 23, kuma tana zaune a anguwar Tunku, ita ma da ke Zariya.
Saurayin da aminiyarsa sun yi bayanin yadda suke shirya safaran ’yan mata zuwa gun ’yan ta’addan masu satar mutane a dajin.
A cewarsu, asirinsu ya tonu ne dalilin rashin dawowar yaran da suka yi safarar tasu zuwa dajin.
Ku kalli cikakkiyar hirarmu da su a wannan bidiyon: