Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na Jihar Sakkwato, ya ce jam’iyyar APC mai mulki a kasar tana kan gabar rushewa nan ba da dadewa ba.
Tambuwal ya yi ikirarin hakan ne a ranar Asabar yayin kaddamar da yakin neman zaben jam’iyyar PDP na zaben Kananan Hukumomi Jihar mai zuwa a ranar 27 ga watan Maris.
- Coronavirus ta yi ajalin mutum 3 a Najeriya, 112 sun kamu
- Za a fafata yakin basasa muddin aka kashe Gwamnan Binuwe – Wike
Aminiya ta samu cewa jam’iyyar APC za ta kaurace wa zaben ne inda ta wassafa dalilai na rashin adalci da cewa wasu daga cikin ma’aikatan hukumar zaben jihar mambobin jam’iyyar PDP ne sannan kuma ana wulakanta gwamnatocin kananan hukomomi ta hanyar hana su hakkokinsu.
Sai da a cewar Gwamna Tambuwal, jam’iyyar APC ta zame jikinta daga zaben ne a sakamakon tsintar kanta da ta yi a cikin matsaloli a matakin kasa da kuma na jihohi.
Gwamnan ya kara da cewa, babu wani abun gwaninta da jam’iyyar APC za ta iya nunawa a matsayin nasarar da ta samu tun hawanta kan mulki a shekarar 2015 kawo yanzu.
“A yanzu haka matsaloli sun rincabe a jam’iyya kuma nan ba da dadewa ba za ta rushe,” in ji gwamna Tambuwal.
A yayin bikin da aka gudanar a Gwadabawa, daya daga cikin Kananan Hukomin Jihar da suke fama da hare-haren ’yan daban daji, Gwamnan ya yi kira ga al’umma da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro hadin kai a kokarin da suke yi na dawo da zaman lafiya a yankunansu.