✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Akwai inda siyasar ubangida ke da haɗari — Wamakko

Siyasar ubangida tana da muhimmanci a inda ake fifita ra’ayin jama’a.

Tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya ce, ba ya zargi ko sukar shugabannin da suka bar mulki.

Wamakko ya ce wanda ya bai wa mulki shekara takwas da suka gabata a Jihar Sakkwato, Sanata Aminu Tambuwal ƙaninsa ne, shi ya kawo shi, don haka ba ya sukar sa a kafafen yada labarai domin wannan ba shi ne tsarin siyasarsa ba.

Sanatan ya bayyana haka ne a hirarsa da BBC Hausa, wanda ya tabo maganar siyasar ubangida a jihar.

Tsohon gwamnan ya ce, “Akwai siyasar ubangida da ke da haɗari da ake yi a wasu wuraren da ba sha’awar jama’a ake kula da ita ba. Amma tana da kyau a inda ake fifita ra’ayin jama’a.”

Sanata Wamakko ya kuma ce, sai gwamnati ta samar da tallafin kuɗi cikin sauki kafin a yi noman da za a samu nasarar ciyar da kasa abinci, kuma akwai buƙatar ta sassauta kuɗin taki da kayan aikin noma.

Ya ce, “Babu yadda za a yi noma ya yi nasara in aka ce ana raba buhun taki daya ga manomi ko kwano biyu.

“Yaya za a yi da wannan? Wannan ba za a kira shi da tallafi ba, wasa ne ake yi da noma, ka ga an ba wa karamar hukuma motar taki biyu, wadda ke da aƙalla mutum dubu 400, yaya za su yi da shi in an raba, ta yaya kowa zai samu abin da zai amfane shi?”

Sanata Wamakko ya ba da tabbacin cewa, mutane za su ga sauyi a tsarin noma domin sun bai wa Shugaban Kasa shawarar yadda za a inganta noma a Nijeriya.

Ya ce, duk al’ummar da take son ta samu nasara a harkar noma dole ne gwamnati ta samar da tallafi a harkar kafin a kai gaci.

Wani mai sharhi a kan al’amurran yau da kullum a Sakkwato, Muhammad Nasir ya shawarci Sanata Wamakko a matsayinsa na jigo kuma jagora ga gwamnatin jihar ya dawo gida (Sakkwato) ya bayar da shawarwarin da yake da su domin sauya harkar noma a jihar.

Muhammad ya ce, a bara gwamnatin ba ta raba takin zamani ga manoman damina ba, haka a bana manoma a Sakkwato sun yi shuka ba tallafin taki daga gwamnatin har, babu wani tsari a bayyane da ke nuna gwamnatin jihar za ta tallafa wa manoma da kayan noman zamani don bunkasa noma.

Ya ce, manoman Jihar Sakkwato suna cikin matsaloli biyu, na farko akwai waɗanda ’yan bindiga suka hana su noman gaba ɗaya, wasu kuma sai sun biya harajin da ’yan bindigar suka ɗora masu kafin su yi noman.

Na biyu kuma inda babu ’yan bindigar suna fama da ƙarancin kayan noma da iri na zamanin da zai bunkasa nomansu.

Ya ce, ya kamata mahunkuntan jihar su duba lamarin da suke ciki don bunkasa harkar noma a jihar.

Mai sharhin ya ce, hukumomin noma a jihar babu wani shiri da aka ga sun ƙaddamar don tallafa wa noma, kuma tsare-tsaren da ake yi a tsakanin gwamnatin jihar da ƙungiyoyin da ke taimaka wa noma duk sun yi sanyi.

Don haka ya kamata a faɗakar da Gwamnatin Jihar Sakkwato a yi wani abu ko a farfaɗo da noma a jihar.

Ya ce, shirin gwamnati na samar da gulaben noma a Kudancin Sakkwato, musamman a qananan hukumomin Kebbe da Silame da Tambuwal da Yabo da Wamakko da kuma gyara gulaben Kalmalo da Talola da Kwakwazo, abu ne mai kyau, amma yaushe ne za a yi wannan aiki bayan gwamnati ta san ana cikin halin da ake buƙatar gaggauta farfaɗo da aikin noman.