Babbar Kotun Tarayya ta kori ƙarar da aka shigar gabanta na neman ta tsige tsohon Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, daga kujerar Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa.
Alƙalin, Mai Shari’a Inyang Ekwo ya kori ƙarar da Ƙungiyar ’Yan APC na Yankin Arewa ta Tsakiya ta shigar ne bisa dalilai da dama.
Ƙungiyar ta yi ƙarar Ganduje da Hukumar Zabe ta Ƙasa (INEC) a gaban kotun da ke Abuja ne, bisa zargin hanyar da aka bi wajen naɗa tsohon shi a kujerar ta saɓa kundin tsarin mulkin Jam’iyyar APC da kuma tsarin dimokuraɗiyya.
Amma Mai Shari’a Ekwo ya bayyana cewa ƙungiyar da ta shigar da ƙarar ba ta da rajista, don haka ba ta da hurumin yin hakan.
- Bidiyon Tsiraici: Hafsat Baby ta shiga hannun Hisbah
- Albashin N70,000: Ma’aikata da gwamnati sun sa hannu kan yarjejeyar karin albashi
Ya ƙara da cewa ƙungiyar ta yi riga malam masallaci, domin ba ta yi amfani da damar yin sulhu a cikin gida na jam’iyyar domin sasanta rikicin ba, kafin zuwa kotu.
Sannan ya ce naɗin shugabannin jam’iyya da jami’an gudanarwarta abu ne cikin gidanta, wanda babu kotun da za ta sa baki a ciki.