Gwamnatin Tarayya ta ce za ta rufe shirin rajistar daukar kananan ma’aikata na musamman 774,000 a fadin Najeriya ranar 21 ga watan Satumbar 2020.
Babban Daraktan Hukumar Kula da Samar da Ayyukan yi ta Kasa (NDE) Nasir Ladan ne ya bayyana hakan a wata sanarwa ranar Litinin.
- Faduwar gini ta kashe mutum shida ’yan gida daya a Kebbi
- Shugabannin Arewa sun bukaci Buhari ya kori hafsoshin tsaro
Gwamnatin ta kuma yi kira ga ’yan Najeriya masu sha’awar aikin da su tuntubi kwamitocin da ke kula da daukar a jihohinsu.
Shirin wani yinkuri ne na samar da ayyukan wucin gadi ga matasa 1,000 a kowacce karamar hukuma domin aiwatar da wasu ayyukan raya kasa a yankunansu.
Wadanda suka sami nasarar aikin za su rika karbar N20,000 a kowanne wata na tsawon watanni uku ta hanyar lambobin sirrinsu na bankuna (BVN).
Ana sa ran shirin zai lakume kimanin Naira biliyan 52 wajen biyan albashi da kuma aiwatar da shirin.
A cewar gwamnati, dole ne wadanda za a dauka su kai shekaru 18 zuwa sama, lafiyayyu marasa nakasa kuma ’yan asali sannan mazauna a karamar hukumomin da suke neman aiki.
Kazalika, ba a bukatar wata shaidar kwalin ilimi kafin a dauki mutum a cikin shirin da zai fara aiki a ranar daya ga watan Oktoba mai kamawa.