Sabbin ma’aikata 774,000 da Gwamnatin Tarayya ta dauka aiki za sa fara aiki daga ranar 5 ga watan Janairun 2021.
Minista a Ma’aikatar Kwadago da Daukar Aiki, Festus Keyamo, wanda ke jagorantar shirin, shi ne ya sanar da haka yana mai cewa komai ya kammala.
“Mun cimma matsayar farawa daga ranar 5 ga Janariu, 2021 amma sai ranar Laraba zan sanar a hukumance a Majalisar Zartarwa ta Kasa.
“Za a yi ne daga watan Janairu zuwa Maris, a cikin rani ke nan. A shirye muke, mun riga mun kawar da duk wani tarnaki”, inji shi.
Gwamnatin Tarayya ta kirkiro shirin ne domin rage radadin annobar COVID-19 ta hanyar daukar kananan ma’aikatan wucin gadi 1,000 daga kowace karamar hukuma na wata uku a kan N20,000 duk wata.
Jinkirin da shirin ya samu
Shirin ya yi ta samun koma baya sakamakon tsattsamar alaka tsakanin Keyamo da tsohon Daraka-Janar na Hukumar Samar da Ayyuka ta Kasa (NDE), Nasiru Muhammad Ladan, wanda Shugaba Buhari ya sallama a makon jiya.
Keyamo ya tabbatar cewa shirin ya samu ‘matsaloli’ da suka haddasa tsaiko wurin fara shi kamar yadda aka tsara tun farko.
“Mun samu ’yan matsaloli har a cikin watan Disamba amma mun riga mun cimma matsayar fara a ranar 5 ga Janair, ranar Talata ke nan.
Ana hasashen ‘matsalolin’, na da nasaba da ja-in-ja kan jagorantar shirin tsakanin Keyamo da Ladan wanda hukumarsa ke karkashi ma’aikatar Keyamo.
Ana zargin Ladan da biye wa Majalisar Tarayya wurin kawo wa ministan matsala, bayan cacar bakin da ministan ya yi da ’yan majalisa a kan shirin.
Mutanen biyu sun yi ta zaman doya da manja kan aiwatar da shirin; ana zargin Ladan wanda tashi ta zo daya da Majalisar Tarayya yana saba umarnin ministan.
Sau biyu Gwamnatin Tarayya na sanar da ranar da ma’ikata su 1,000 daga kowacce daga Kananan Hukumomin Najeriya 774 za su fara aiki ana dagewa.
Duk da cewa an fitar da Naira biliyan 26 na biyan ma’aikatan da kuma sayen kayan da za su yi aiki da su, shirin ya gagara fara aiki.
Jaridar the Nation ta ruwaito cewa a ranar Lahadi, Keyamo ya shaida mata cewa za a fara aikin a cikin watan Janairu, kuma za a sanar a hakan a lokaicn zaman Majalisar Zartarwa ta Kasa (FEC).
A cewarsa, shirin zai tafi ba tare da wata tangarta ba tunda an cire Ladan daga mukaminsa.
Ya ce bankunan da Shugaban Kasa ya amince da su ne kadai za a yi amfani da su wurin biyan ma’aikatan kudadensu.