Shugaba Muhammadu Buhari ya sallami Darakta-Janar na Hukumar Samar da Ayyyuka ta Kasa (NDE), Nasir Muhammad Ladan Argungu daga mukaminsa.
Wani babban jami’in hukumar ta NDE ya tabbatar wa Aminiya cewa an umarci Minista a Ma’aikatar Kwadago da Daukar Aiki, Festus Keyamo ya nada Darakta-Janar na riko daga cikin Manyan Daraktocin hukumar.
- Najeriya na leken asirin wayoyin ’yan kasarta —Rahoto
- Ayyukan noma: Hukumar NDE na horas da mutum 100
- Ma’aikata 774,000: Keyamo ya koma gefe kawai
Ba a dai bayyana dalilin sallamar Nasiru Ladan daga mukaminsa ba, amma majiyarmu ta ce ba zai rasa nasaba ba da tafiyar hawainiya a daukar ma’aikata 774,000 daga kananan hukumomin Najeriya 774.