Gwamnatin Tarayya ta ce ta bullo da wani sabon shiri da ta yi wa lakabi da GAP wanda zai mayar da hankali wajen samar wa da matasa masu digiri ayyukan yi na wucin gadi.
Shugaban Hukumar Samar da Ayyukan yi ta Kasa (NDE), Abubakar Nuhu Fikpo ne ya sanar da hakan ranar Talata a birnin Uyo na Jihar Akwa Ibom yayin da yake duba wani taron bayar da horo kan sana’o’in na kwana biyar a Jihar.
- An kama mutum 19 bisa zargin garkuwa da mutane a Jigawa
- Taliban ta kafa sabuwar gwamnati a Afghanistan
A cewarsa, hukumar za kuma ta samar wa da matasa 2,572 wadanda suka kammala karatu a manyan makarantun Najeriya su sami aiki a ma’aikatun gwamnati daban-daban.
Hakan na zuwa ne kwanaki kadan bayan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da shirin “Nigeria Jubilee Fellows”, ya kuduri aniya samar wa da mutum 20,000 ayyukan yi a kowacce shekara.
A cewar kakakin NDE, Edmund Onwuliri cikin wata sanarwa ranar Talata, matasan da suka kammala digiri ne kuma suka kammala yi wa kasa hidima za su amfana da shirin na GAP.
Shirin dai ana sa rai zai taimaka wa matasan wajen saukin samun aiki da kuma kauce wa shafe tsawon lokaci ba su sami aiki ba saboda karancin kwarewa.
Sanarwar ta ce shirin wanda zai kasance na tsawon watanni uku a karon farko, zai zama na wata shida ne.
Ya kara da cewa, “A lokacin da suke aikin, ana sa ran za su sami kwarewa a ma’aikatun da za a tura su, wanda zai iya kai wa ga a rike su a wajen ayyukan nasu.”