✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Saudiyya za ta koma aiki da motoci masu amfani da lantarki

Gwamnatin Saudiyya ta kuduri aniyar ware kaso biyar na wuraren ajiye ababen hawa don motoci masu amfani da wutar lantarki a fadin kasar. Ma’aikatar Raya…

Gwamnatin Saudiyya ta kuduri aniyar ware kaso biyar na wuraren ajiye ababen hawa don motoci masu amfani da wutar lantarki a fadin kasar.

Ma’aikatar Raya Birni da Karkara ta kasar ta ce za ta samar da wuraren cajin motocin masu amfani da lantarki a wuraren da aka ware don ajiyar motocin.

Jaridar Al-watan ta kasar ta rawaito cewa hakan na kunshe cikin sabon daftarin dokar da ma’aikatar ta fitar.

Ma’aikatar ta karkasa wuraren cajin motocin zuwa rukuni uku: na farko, shi ne na motoci masu jimawa a wurin ajiya wanda ya hada wuraren ajiye motoci da ke kusa da gidajen jama’a da ofisoshi da tashar jirgin kasa da tashoshin motocin jigilar fasinjoji.

Rukuni na biyu kuma an ware ne don masu ajiye motoci na gajeran lokaci da suka hada da wuraren kasuwanci da shagunan tireda da dakunan taro da otel-otel.

Na uku shi ne na gefen titinan da ake hadahadar kasuwanci da manyan hanyoyi da gidajen mai.

Ma’aikatar ta ce ta fito da sabbin tsare-tsaren ne don tafiya da zamani da kawata birninta ta yadda zai yi gogayya da manyan biranen duniya da kuma komawa amfani da ababan hawa masu amfani da wutar lantarki a madadin man fetur.

Manufar ta kuma hada da inganta lafiyar jama’a ta hanyar kauce wa gurbatacciyar iskar da ake shaka daga ababan hawa masu amfani da fetur.