✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Saudiyya za ta jagoranci taron tara wa ƙasashen Afirka 6 kuɗi

Ƙasashen yankin Sahel da na Tafkin Chadi sun shafe fiye da shekara 10 suna fama da rikice-rikice.

Saudiyya ta ƙudiri aniyar agaza wa al’ummomin ƙasashen Nijeriya da Nijar da Chadi da Kamaru da Burkina Faso da Mali da ke buƙatar tallafin jin ƙai.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwar da Babban Jami’i a Cibiyar Bayar da Tallafi ta Sarki Salman, Domta Abdullah Al Rabeeah ya fitar a ranar Juma’a.

Cibiyar ta ce za ta tallafa wa ƙasashen ne ta hanyar shirya wani taro domin tara wa ƙasashen kuɗi wanda za a gudanar ranar 26 ga watan Okbota na bana.

Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi ƙiyasin cewa kusan mutum miliyan 33 ne ke buƙatar tallafi a yankin, ciki har da mutum miliyan 11 da aka raba da muhallansu a yankunan Sahel da Tafkin Chadi.

Taron — wanda Cibiyar Bayar da Agaji da Sarki Salman da Ƙungiyar Ƙasashe Musulmai ta Duniya, OIC da Ofishin Kula da ’Yan Gudun Hijira na Majalisar Ɗinkin Duniya  — za a shirya shi ne da nufin tara kuɗi da kayan agaji don magance matsalar jin kai da ake fuskanta tare da kare fararen hula a ƙasashen.

Ƙasashen yankin Sahel da na Tafkin Chadi sun shafe fiye da shekara 10 suna fama da rikice-rikice, lamarin da ya haifar da matsalolin zamantakewa da na tattalin arziki da asarar rayuka.

Sanarwar ta ce ’yan gudun hijira da mutanen da suka rasa muhallansu ne kan gaba cikin waɗanda za su samu tallafin.