✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Saudiyya za ta gina katafariyar makarantar wasanni

Ana sa ran za ta kasance daya daga cikin makarantun wasanni mafi girma a duniya.

Gwamnatin kasar Saudiyya ta amince da kafa makarantar koyon harkokin wasanni da zimmar gano tare da horar da zakakuran matasan kasar ta fuskar wasanni.

Ana sa ran makarantar mai suna ‘Mahd Sports Academy’ za ta kasance daya daga cikin makarantun wasanni mafi girma a duniya cikin shekara 10 masu zuwa.

Za a gina ta da burin samar da sabuwar al’ummar Saudiyyar mai kwarewa a harkokin wasanni.

Makarantar, wacce aka kaddamar a watan Yulin bara ta samu yabo daga manyan masu ruwa da tsaki a sha’anin wasanni na duniya, ciki har da Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA), Gianni Infantino, da kocin ’yan wasan kasar Italiya, Roberto Mancini da kwararren kocin nan, José Mourinho.

A lokacin kaddamarwar, Ministan Wasannin Saudiyya, Yerima Abdulaziz Bin Turki Al-Faisal, ya ce, “Wannan aikin, mafarkin kasar ne ya zama gaskiya, duba da a yanzu kasar za ta mayar da hankali kacokam wajen samar da zakakuran matasan Saudiyya da za su yi gogayya a duniya su zama abin alfaharin kasar.”

Daga sauye-sauyen da kasar ta fito a ’yan shekarun nan su sun hada da kyale mata su fara tuka mota da kuma shiga harkokin wasanni a dama da su.

Makarantar ta Mahd Sports Academy za ta zakulo yara da ’yan mata masu basira ’yan shekara shida zuwa 12 a kasar.