✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Saudiyya za ta bayar da damar yin shagali a kasar

Kasar Saudiyya ta bayyana shirye-shiryen da take yi na bunkasa bangaren nishadi a kasar, wanda ya hada da bai wa gidajen abinci takardar izinin gudanar…

Kasar Saudiyya ta bayyana shirye-shiryen da take yi na bunkasa bangaren nishadi a kasar, wanda ya hada da bai wa gidajen abinci takardar izinin gudanar da nishadi kai-tsaye, kamar yadda ake yi a kasashen Turai.

Shirin da za a kaddamar a 2019 zai kunshi shigo da taurari kamarsu Jay Z da Dabid Beckham.

Saudiyya ta bayyana shirye-shiryen ne a daidai lokacin da ake ci gaba da ce-ce-ku-ce kan kisan gillar dan jaridar nan Jamal Khashoggi da ake zarginta da shi.

Kokarin da ake yi na mayar da Saudiyya wani yankin nishadantarwa na daya daga cikin abubuwan da Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman ke yi, wanda lamarin kisan Jamal Khashogji ya yi matukar bata wa suna.

Ko a watan Fabrairun bara  Saudiyya ta ce za ta ware Dala biliyan 64 domin bunkasa masana’antunta na nishadantarwa a cikin shekara 10 masu zuwa.

Shugaban Hukumar Kula da Harkokn Nishadi ta kasar ya ce an tsara shirya abubuwa kimanin 5,000 a bana da suka kunshi bikin cashewa na Maroon 5 kamar irin wanda ake gudanarwa a Amurka.

Akwai kuma bikin cashewa na Cirkue du Soleil irin wanda ake gudanarwa a kasashen Turai.

Tuni dai Saudiyya ta fara aikin gina wajen cashewa a birnin Riyadh.

Shirin zuba jarin na cikin sababbin manufofin bunkasa tattalin arziki da ake kira Bision 2030 wanda Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman ya kaddamar shekara kusan uku da suka gabata.