Gwamnatin Saudiyya ta zartar da hukuncin kisa ga wasu sojojinta biyu, ciki har da wani babban matuƙin jirgin soji, kan laifin cin amanar ƙasa.
Kamfanin Dillancin Labaran Saudiyya (SPA) ya ce an zartar wa Pilot Colonel Majid bin Moussa al-Balawi da Chief Sergeant Youssef bin Reda al-Azouzi hukuncin kisa ne a birnin Da’if a ranar Alhamis.
- Gwamnati ta lashe amanta kan dawowar jiragen Daular Larabawa
- ’Yan ta’addan Boko Haram sun kashe manoma 5, sun sace 3 a Borno
Rahoton ya ce kotu ta kama Pilot Colonel Majid bin Moussa al-Balawi ne da laifin “cin amanar soji, kin kare ƙasa da kuma bijire wa umarnin soji.”
Chief Sergeant Youssef kuma an same shi da laifin babban cin amanar kasa da ta aikin soji, da sauransu.
SPA bai yi ƙarin bayani a kan laifukan sojojin ba, ko da yake Saudiyya ba ta fiye fitar da bayanai game da abin da ya shafi rundunar tsaronta ba.
Duk da cewa ba a fiye yanke wa sojoji hukuncin kisa a Saudiyya ba, wanda aka yi ranar Alhamis ya sa adadin mutanen da aka zartas wa hukuncin kisa a ƙasar a bana karuwa zuwa 106.
A bara mutum 147 aka zartar wa hukuncin, ciki har da wasu 81 da aka kashe a rana guda kan laifukan ta’addanci, wanda ya jawo ce-ce-ku-ce daga wasu ƙasashen duniya.
Rahoton kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International na shekarar 2022 ya nuna Saudiyya ce ta uku a jerin kasashe masu zartas da hukuncin kisa, bayan China da Iran.