Kasar Saudiyya ta zartar da hukuncin kisa a kan wadansu sojojinta uku da aka kama da laifin cin amanar kasa.
An zartar wa sojojin hukuncin kisan ne bayan kama su da laifin hadin baki da makiyan kasar da manufofin rundunar sojinta.
- Ba zafin kai kuka fi mu ba —Matawalle ga ’yan Kudu
- El Clásico: Yadda za a kece raini tsakanin Real Madrid da Barcelona
- Ganin ’yan bindiga ya fi sauki a kan ganin Buhari – Sheik Ahmad Gumi
- Abin da ya faru a tarzomar Gidan Yarin Bauchi
Sanarwar da Ma’aikatar Tsaron Saudiyya ta fitar bayyana sunayen sojojin da aka zartar wa haddin a ranar Asabar, da amincewar Sarki Salman.
An zartar wa sojojin haddin ne a harabar Hedikwatar Sojin Kasar da ke kusa da iyakanta da makwabciyarta, kasar Yemen.
Saudiyya na jagorantar rundunar hadin gwiwar kasashen Larabawa da ke yakar ’yan tawayen Houthi a Yemen masu samun goyon bayan Iran.
A baya-bayan nan, mayakan na Houthi sun tsaurara hare-harensu a kan Saudiyya, musamman ta hanyar amfani da jiragen yaki marasa matuka.