✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Saudiyya Ta Yafe Wa ’Yan Yawon Bude Ido Bizar Umrah

Hukumomin kasar sun yi haka ne don ba mutane da yawa damar gudanar da wanan aiki na ibada cikin sauki.

 Ma’aikatar Kula da Aikin Hajja da Umrah ta kasar Saudiya ta sassauta wa masu zuwa kasar yawon bude ido yin Umrah ba tare da bizar Umrah ba.

Hukumomin kasar sun yi haka ne don ba mutane da yawa damar gudanar da wanan aiki na ibada cikin sauki.

Abin da kawai ake bukata daga mai niyya daga kasashen shi ne cikakkiyar insorar lafiya wacce ta hada da ta kudin rigakafin cutar COVID-19 da jinyar ta a Saudiyya in ya kamu.

Sai kuma insorar hadarin da ka iya nakasta mutum ko mutuwa da kuma tanadin kudin maganin kaka-ni-kayi idan an samu jinkirin tashin jirgi ko soke tashinsa baki daya.

Wasu karin shruddan su ne takardar shaidar wurin zama da ta aikin yi da tikitin dawowa da takardar shaidar ajiyar banki da ke nuna karfin aljihun mutum da kuma cikaken bayaninsa.

’Yan kasashe 49 ne aka ba wannan dama ciki har da kasashen Birtaniya da Amurka da kuma kasashen da ke cikin tsarin tafiye-tafiye na Schengen.

Sauran kasashe kamar Najeriya da ire-irensu, sai dai su nemi izini kai-tsaye daga Ofishin Jakadancin Saudiyya da ke kasashensu.