Ma’aikatar Aikin Hajji ta kasar Saudiyya ta sanar da ware wa Najeriya kujeru 95,000 a yayin Aikin Hajjin shekara ta 2024 mai zuwa.
An sanar da haka ne yayin wata tattaunawa da aka yi tsakanin Hukumar Aikin Hajji ta Najeriya (NAHCON) da Ma’aikatar Aikin Hajji da Umara ta Saudiyya a ranar Talata.
- ‘Matatar man Ɗangote za ta fara aiki a watan Nuwamba’
- Zaben 2023: Atiku ya ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Ƙoli
Tattaunawar dai na alamta fara shirye-shiryen Aikin Hajjin baɗi a hukumance.
Taron tattaunawar ya kuma sami halartar Shugaban kwamitin Aikin Hajji na Majalisar Wakilai, Jafar Mohammed da wakilin Shugaban kwamitin harkokin waje na Najeriya, Sanata Abubakar Sani Bello da kuma Jakadan Najeriya a Saudiyya, Bello Abdulkadir.
Mataimakin Darakta mai kula da yada labarai na NAHCON, Mousa Ubandawaki ne ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa ranar Talata.
Daga cikin abubuwan da aka amince da su yayin tattaunawar shi ne Najeriya za ta kammala dukkan shirye-shiryen aikin a cikin kwanaki 120 masu zuwa.
Tun da farko dai sai da Shugaban NAHCON, Zikrullah Kunle Hassan ya bukaci gwamnatin Saudiyya da ta daure ta dawo wa Najeriya canjin kudin abinci da na tantinan da ba a yi amfani da su ba yayin Aikin Hajjin da ya gabata a Muna.
Ya kuma roki kasar da ta taimaka ta daina ba alhazan Najeriya abinci a Muna da Arafat, domin a ba gwamnatin Najeriya damar girka musu irin abincin da suka saba da shi a gida.