Hukumar Kula da ‘Yan Najeriya Mazauna Kasashen Waje (NiDCOM), ta sanar cewa a halin yanzu Saudiyya na tsare da kimanin ’yan Najeriya 800 da ake zargi da laifuka daban-daban.
NiDCOM ta bayyana hakan ne yayin da take gargadin ‘yan Najeriya da su ti taka-tsantsan domin Saudiyya ta tsaurara matakan dakile bakin haure a kasar.
- APC ta bukaci Buhari ya mutunta umarnin Kotun Koli kan wa’adin tsofaffin kudi
- Mutum 15 sun shiga hannu kan fasa banki a Akwa Ibom
Sanarwar da NiDCOM ta fitar, ta ce hankalinta ya karkata ga wata sanarwa da Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya ya fitar, kan mahukuntan Saudiyya.
NiDCOM ta ce Saudiyya ta sanar da kara kaimi wajen murkushe baki ’yan kasashen waje da ba su da izinin shiga kasarsu.
Sanarwar ta bayyana cewa, tsakanin watan Oktoba zuwa Disamba 2022, masarautar Saudiyya ta kara kaimi don dakile kwararar bakin haure.
A cikin wasikar da ta aike wa Gwamnatin Tarayya, Saudiyya ta bayyana cewa akwai baki kimanin 45,458 a kasar da ake zargi da aikata laifuka da suka hada da keta ka’idojin zama, yunkurin ketare iyaka da bakin haure da kuma laifukan da suka shafi kwadago.
NiDCOM ta ce duk da cewa ofishin jakadancin Najeriya da ke Saudiyya na tattaunawa kan lamarin, ya bukaci ‘yan Najeriya da su guji karya dokokin wasu kasashen da suke zaune.
Sai dai hukumar ta yi kira ga ‘yan Najeriya da ke son zuwa wasu kasashe da suke ke bin hanyoyin da suka dace.