✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Press To Play

Saudiyya ta soke gwajin COVID-19 da yawan shekaru a Hajjin 2023

Saudiyya ta kuma ware wa maniyyatan Najeriya gurabu 90,000 don sauke farali a 2023

Masarautar Saudiyya ta soke sharadin yin gwajin kwayar cutar COVID-19 da kayyade shekaru ga maniyyata aikin Hajjin 2023.

Ma’aikatar Aikin Hajji da Umrah ta Saudiyya ta kuma ware wa maniyyatan Najeriya gurabu 90,000 don sauke farali a 2023 — adadin da Najeriya ke samu gabanin bullar cutar COVID-19.

“Ma’aikatar ta kuma ba wa Hukumar Aikin Hajji ta Najeriya (NAHCON) izinin zabo kamfanin da zai kula da ciyarwa, sufuri da samar da tantuna a Mina da sauran hidindimu ga maniyyatan Najeriya, musamman a ranakun aikin Hajji,” in ji hukumar.

Mataimakin Daraktan Yada Labaran NAHCON, Mousa Ubandawaki, ya ce za Ma’aikatar da NAHCON za su kammala batun samar da masaukin maniyyyata a ranar 10 ga watan Fabrairun 2023, sauran shirye-shiryen kuma za a kammala su a ranar 24 ga watan Janairu.

Ubandawaki ya ce, Darakta-Janar na Ma’aikatar Aikin Hajji da Umrah na Saudiyya, Bahauddeen bin Yusuf Alwani, ne ya sanar da hakan a ganawarsu ta bidiyo da Shugaban NAHCON, Zukrullah Kunle Hassan.

Alwani ya ce, “Wajibi ne a kammala mika bayanan kamfanonin jiragen sama da za su yi jigalar maniyyatan Najeriya da wuri kafin fara jigalar aikin Hajjin 2023,”  in ji sanarwar da Ubandawaki ya fitar.

A nasa bangaren Shugaban NAHCON ya iy godiya ga Saudiyya bisa dawo wa Najeriya da yawan gurabun maniyyatan zuwa 90.

Sai dai ya bukaci ta bar NAHCON ta kula da ciyar da alhazai a ranakuna aikin Hajji, domin guje wa abin takaicin rashin ciyar da alhazan Najeriya yadda ya kamata da kamfanin da aka ba wa aikin ya yi a lokacin aikin Hajjin 2022.

Karin gurabun maniyyata da Saudiyya ta yi wa Najeriya a Hajjin 2023, na nufin ta kara adadin zuwa yadda yake bayan rage shi zuwa rabi sakamakon bullar cutar COVID-19.

Bullar cutar ta sa aka hana maniyyata daga wajen Saudiyya yin aikin Hajji a shekarar 2020, kafin daga bisani a 2021 da 2022 aka rage shi zuwa rabin maniyyata (45,000 daga Najeriya).