Sarki Salman Bn Abdulaziz na Saudiyya, ya bayar da umarin takaita raka’o’in sallolin taraweeh a masallatan Harami na Makkah da Madinah yayin watan Azumin bana.
Shugaban masu da kula masallatan biyu, Sheikh Abdul Rahman Al-Sudais ne ya sanar da hakan da cewa za a rage yawan raka’o’in zuwa daga 20 a aka saba yi a lokutan baya.
- A dakata da shiga I’tikafi a Azumin bana — Sarkin Musulmi
- Gwamnati ta kara wa’adin hutun dalibai a Kano
Jaridar Saudi Gazette ta ruwaito Sudais yana cewa za a rika gabatar da sallolin ne ta hanyar kiyaye matakan da mahukunta suka gindaya na dakile yaduwar annobar Coronavirus.
Sudais wanda kuma shi ne jagoran limaman masallatan biyu, ya ce za su ci gaba da yin duk wata mai yiwuwa wajen samar da kyakkayawan yanayi domin gudanar da ibadu cikin aminci.
A bana hukumomin Saudiyya sun amince a gudanar da Umarah yayin da kuma suka hana I’itikafi da bude baki a masallatan biyu yayin watan mai alfarma.
Hukumomin sun kammala duk wani tanadi na dawainiya da masu Umarah akalla 50,000 da kuma masu ibada dubu dari a watan Azumin bana, inda za a tabbatar kowanensu ya karbi allurar rigakafin cutar Coronavirus.
A Talatar makon gobe ce al’ummar Musulmi a fadin duniya ke fatan fara Azumin watan Ramadan.
A Azumin bara ne hukumomin Saudiyya suka dakatar da duk wasu sallolin farilla da na nafila da kuma Umarah yayin da annobar Coronavirus ke ci tamkar wutar daji.