Masarautar Qasar Saudiyya ta nuna kyakkyawan misali kan halayyar huldar dangantakar difilomasiyya ta duniya wajen mutunta juna da girmamawa, a yayin da kai ziyarar ban girma ga ofishin Najeriya a Birnin Madina don neman afuwa bisa ga abinda ya faru da wasu ‘yan Najeriyar a makon jiya na musgunawa daga jami’an tsaron qasar ta Saudiyya.
Mataimakin Gwamnan Madina, Dakta Wehab As-Silhy, wanda tare da rakiyar Mataimakin Ministan Ayyukan Hajji da Umrah na sashen Madina, Dakta Abdurrahman Bijawi, inda suka buqaci afuwar Najeriya a madadin fadar qasar a kuma lokacin da ya ziyarci wadanda lamarin ya shafa Otal din Wefada Al Zahra dake kan titin Al-Salam a unguwar Markaziyya a Madina.
A yayin zantawa da manema labarai bayan ziyarar, mataimakin ministan ya bayyana cewa sun yi nadamar faruwar lamarin, sannan ya bada tabbacin cewa za a kiyaye faruwar hakan anan gaba. Yana mai cewa idan har akwai abinda daular saudiyyar ba za ta lamunta ba, to bai wuce tozarta maniyyata ba.
“A madadin Mai Martaba Sarki, da Gwamnan Madina tare da dukkannin shugabannin masarautar, muna qara nuna alhininmu bisa faruwar lamarin, sannan muna neman afuwa sannan muna qara jaddada muku cewa Saudiyya ba zata sake barin haka ta faru baa nan gaba” Haka kuma ya sake bayyana manufar gwamnatin qasar cewa, za ta cigaba da baiwa dukkan maniyyata cikakken kulawa tare da ba su tsaro a tsawon zamansu na kwanakin hajji baki daya.
A yayin da yake mayar da jawabi a madadin Najeriya, Babban Jami’in Kula da Harkokin Jakadanci dake Riyadh, Ambasada Umar Z. Salisu ya nuna jin dadinsa ga wannan mataki da Gwamnatin Saudiyya ta dauka cikin gaggawa bayan samu qorafinmu akan faruwar lamarin, “A gaskiya mun yi matuqar farin ciki game da matakin da Gwamnatin Saudiyya ta dauka wajen yin bincike don hukunta wadanda ka samu da laifin, sannan da kuma alqawarin baiwa alhazan Najeriya kulawa ba tare da samun wata fargaba anan gaba wajen gudanar da ayyukan hajji ba,” In ji shi.
A wani yanayi da ba a saba gani ba a yayin wannan ziyarar ita ce yadda aka gurfanar da jami’an da suka yi wannan aika-aika ga maniyyatan Najeriya guda biyu, inda suka nemi afuwa bisa laifin nasu a gaban Mataimakin Gwamnann da dukkan tawagar.
Wannan karamci ta Saudiyya dai ita ce karo na farko da shugabannin qasar suka nemi afuwa game da laifin da ta aikata, sannan kuma babbar nasara ce ga Hukumar Alhazai ta Qasa wanda kodinetanta na Madina, dakta Mohammed Bello Tambuwal ya rubuta takardar qorafi ga gwamnatin saudiyyar akan faruwar lamarin.