Gwamnatin kasar Saudiyya ta kwashe wasu daga cikin ’yan Najeriya da suka makale a yakin da ya barke a Sudan zuwa kasarta.
Minista a Ma’aikatar Harkokin Waje ta Najeriya, Zubairu Dada, ya ce Saudiyya ta tura jiragen ruwa da suka kwashe ’yan Najeriya zuwa birnin Jeddah na kasarta, bayan barkewar yaki a Sudan.
Ma’aikatar ta ce daga bisani za a maido da ’yan Najeriyan da aka kai Saudiyya gida, kuma gwamnatin Tarayya na kokarin ganin cewa babu dan Najeriya ko daya da ya rage a Sudan kafin cikar wa’adin awa 72 da bangarorin da ke yaki da juna suka bayar na tsagaita wuta.
Ta bayyana cewa a kokarinta na kwashe ’yan Najeriya da suka makale bayan barkewar yakin, Gwamnatin Tarayya ta kashe Naira miliya 552 kan daukar hayar motocin da za su fitar da su zuwa iyakar Sudan da kasar Masar.
- Tankar mai ta yi bindiga ‘yan sa’oi bayan gobarar Kasuwar Katako ta Bodija
- Zulum ya kaddamar da gidajen ’yan gudun hijira a Gwoza
Ministan Harkokin Waje na Najeriya, Geoffrey Onyema, ya ce an dauki hayar bas-bas 40 da za su kwashi ’yan Najeriya daga Khartoum, babban birnin Sudan zuwa iyakar kasar Masar da ke Aswan, inda za su hau jirgi zuwa gida.
“Dala miliyan 1.2 (Naira miliyan 552) aka caje mu kan bas 40 da muka nema; Mun samu bas guda 40 na alfarma da za su dauki ’yan Najeriya (daga Khartoum) zuwa iyakar kasar Masar.
“Sanin kowa ne cewa tabbas irin wannan yanayi akwai wadanda za su yi amfnai da rikicin Sudan wajen tatsar jama’a,” in ji Oyema.
Ya ce duk da cewa, “Mun ga yadda aka kai wa ayarin motocin kasar Faransa hari da sauransu, amma dole mu yi abin da za mu yi domin kubutar da rayukan ’yan kasarmu.”
Da yake karin haske, Minista a Ma’aikatar, Zubairu Dada, ya ce gwamnati ta tanadi matakan tsaro da za su tabbatar da tsaron ’yan Najeriyan da za a yi jigilarsu zuwa Masar.
Ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya na yin dukkan mai yiwuwa wajen ganin an gama kwashe ’yan Najeriya cikin sa’a 72 da gwamnatin Sudan ta bayar na tsagaita wuta.
“Ba mu da matsala da wa’adain awa 72 da gwamnatin ta bayar kuma mun tattauna da bangarorin da abin ya shafa, kuma sun ba mu hadin kai,” in ji shi.
Ya ci gaba da cewa “Za a kwashe ’yan Najeriya ne a rukuni-rukuni domin tabbatar da tsaron lafiyarsu; kuma Alhamdulillah babu dan Najeriya ko daya da ya rasa ransa.”