Saudiyya ta koro mutum bakwai daga cikin maniyyatan aikin Hajjin da suka bi jirgin karshe daga Jihar Kano ranar Alhamis.
Hukumomin Saudiyya sun tiso keyar maniyyatan ne bayan saukarsu a filin jirgi da ke Jiddah, kan zargin amfani da jabun biza, sa’o’i kadan kafin wayewar garin ranar tsayuwar Arafa.
- Kurewar wa’adin Saudiyya: Zargin cuwa-cuwar biza ya dabaibaye NAHCON
- BIDIYO: Yadda Matan Kano Ke Gogayya Da Maza A Harkar Kwallon Kafa
Aminiya ta gano biyar daga cikin maniyyatan ’yan jirgin yawo ne, sauran sauran kuma sun bi ta hannun Hukumar Kula da Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano ne.
Daya daga cikin maniyyatan da aka dawo da su, Dahiru ,Musa ya shaida wa Aminiya cewa bai san cewa jabun biza yake dauke da ita ba sai da ya isa Kasa Mai Tsarki.
“Da muka isa Kasa Mai Tsarki ana yi mana bincike sai aka ware ni wuri daya daga nan aka yi magana da Jami’an Hukumar Alhazan Najeriya inda suka shaida min halin da ake ciki.
“An dauki tsawon lokaci ana kokarin warware lamurran amma abin bai yiwu ba a karshe dai aka dauko mu mu bakwai aka dawo da mu Jihar Kano.”
Ya bayyana takaicinsa inda ya ce “Ai na shiga cikin bakin ciki mai yawa.
“A matsayinka na Musulmi a ce ka je har Kasa Mai Tsarki kana ganin abokan tafiyarka suna tafiya Makka amma kai kana ji kana gani a dawo da kai gida, wannan abin bakin ciki da takaici ne ba kadan ba.”
Dahiru ya sha alwashin daukar matakin shari’a a kan kamfanin da ya yi jigilar tasu.
“Tunda muka dawo masu kamfanin suke nema na, amma na ki yarda saboda ba na son jin wani abu daga gare su, sai dai mu hadu a kotu. Haka kuma ba zan kyale su haka ba sai mun je ga Ofishin Jakadancin kasar Saudiyya domin a tantance yadda lamarin gaskiya yake domin a wanke ni saboda kada na sami matsala wajen shiga kasar a nan gaba.”
Shugaban Hukumar Jin dadin Alhazan Jihar Kano, Muhammad Abba Danbatta, ya tabbatar da batun dawo da maniyyatan, sai dai ya bayyana cewa maniyyatan biyu da suke da’awar, Hukumarsu ba ta san da tafiyarsu ba.
“Lokacin da na sami wannan labari misalin karfe 2:00 na dare na je Filin Sauka da Tashin Jirage na Malam Aminu Kano don ganawa da maniyyatan.
“Duk da cewa alhazan biyu namiji da mace suna sanye da kayan alhazanmu da jakunkunanmu, sun kuma ce daga Karamar Hukumar Sumaila suka biya kudinsu, amma ba alhazanmu ne na gaskiya ba.
“Na kira Shugaban Alhazai na Sumaila amma dukkaninsu shi da su ba su san juna ba.
“Mun gano cewa wani daga cikin ma’aikatanmu ne mai suna Abdurrahman ya karbi kudinsu ya cusa su cikin alhazanmu tare da yi musu jabun biza.
“Ko rasidin da ya ba su da ke dauke da sunan hukumarmu na jabu ne,” acewar Abba Danbatta.
Ya cea yanzu haka sun mika lamarin ga hukumar da ta dace don fadada bincike wanda kuma idan har aka kama ma’aikacinn nasu da laifi to zai fuskanci fushin kuliya.
“Mun damka lamarin ga Hukumar Shuge da Fice ta Kasa don fadada bincike.
“Kasancewar a yanzu haka ba a samun shi wanda ake zargi da wannan aiki a wayarsa, za a ci gaba da neman sa.
“Da zarar an same shi da laifi zai fuskanci hukunci daidai da laifin da ya aikata,” kamar yadda ya bayyana.