Masarautar Saudiyya ta sallami shugaba da wani babban jami’i a wani kamfanin kula da hidimar alhazai a kasar.
Ma’aikatar Aiki Hajji ta Saudiyya ta ce ta sallami shugabannin kamfanin tare da fara binciken su ne bayan korafe-korafen jami’an ma’aikatar kan rashin ingancin ayyukan kamfannin a aiki Hajjin bana.
- Harin Kuje: An kama ’yan sanda na waya da ’yan ta’addar da suka tsere
- Rasha ta samu Dala 24bn daga sayar wa China da Indiya iskar gas
A safiyar Alhamis ce Ma’aikatar ta sanar cewa ta dauki matakin ne bayan wani zama da ta yi da majalisar daraktocin kamfanin, sakamakon rahohon da jami’an ma’aikatar masu kula da ingancin ayyuka.
Ma’aikatar ta ce za ta tsaurara wajen sanya ido kan ingancin ayyukan kamfanonin da aka ba wa aikin yi wa alhazai hidima domin hukunta masu kunnen kashi nan take.
Ta bayyana cewa ba za ta lamunci kowane irin kwange ba wajen gudanar da ayyukan hidima ga alhazai, Bakin Allah.
“Jami’anmu na yin zagaye domin tantance ingancin ayyukan hidimar da ake yi wa alhazai, tare da daukar mataki nan take a kan duk wani rahoto ko korafi.
“Wannan na daga cikin matakan da muka dauka domin tabbatar da ingancin hidima da tsaron lafiyar alhazai,” inji sanarwar.
Hakan, a cewarta, zai tabbatar aminci da gamsuwa da kuma kwanciyar hankalin alhazai da suka zo Kasa Mai Tsauki domin gudanar da ibadar Hajji mai daraja.
Aikin Hajji, wanda a bana ke farawa a ranar Alhamis, yana daga cikin rukunnan Musulunci guda biyar.
A wannan karon, Musulmi akalla miliyan daya daga fadin duniya ne za su gudanar da ibadar.
Wannan ne kuma karo na farko a cikin shekara uku da aka ba da dama ga maniyyata daga ko’ina a fadin duniya su shiga Saudiyya domin gudanar da aikin.
Shekara biyu da suka gabata an rika takaita yawa mahajjata zuwa kasa da mutum 70,000 a duk shekara, saboda bullar cutar COVID-19.