Saudiyya ta haramta aure ga mutane ’yan kasa da shekara 18 da haihuwa a kasar ta.
Sabuwar dokar da Ministan Shari’ar kuma Shugaban Majalisar Shari’ar Saudiyya, Sheikh Walid Al-Samaani ya rattaba wa hannu ta sanya shakera 18 a matsayin mafi karancin shekarun ma’aurata a kasar.
- ’Yan bindiga na haurowa Najeriya daga Mali — Makinde
- Dogo Gide: Mutumin da ya hallaka Buharin Daji
- Mace-macen da suka fi girgiza Najeriya a 2020
“Kafin a daura aure wajibi ne a tabbatar cewa auren mai shekara kasa da 18 ba zai cutar da shi ko ita ba kuma shi ne mafi aula ga na mijin ko matar,” inji Ministan.
Umarnin da Ministan ya aike wa kotunan kasar, ya kuma wajabta mika bukatar izinin daurin aure ga kotuna na musamman domin tabbatar da cike ka’idojin Dokar Kare Hakkin Kananan Yara baya ga sauran dokokin kasar.
Karon farko ke nan da Gwamnatin Saudiyya ta yi dokar hana auren kananan yara (‘yan kasa da shekara 18) a kasarta.
A farkon shekarar 2020 kasar ta haramta aurar da da ’yan kasa da shekara 15 a kasarta.
An yi dokar ta farko ce bayan ta samu amincewar kashi biyu bisa uku na ’yan Majalisar Shura ta Kasar.
Dokar farkon ta amince wa ’yan kasa da shekara 18 su yi aure idan suka samu izini daga kotuna na musamman.
Amma sabuwar da aka sanya wa hannu a ranar Talata ta hana wa duk ’yan kasa da shekara 18 yin aure, ta kuma sanya hukunci ga duk wanda ya saba dokar.
Bincike ya nuna kashi daya bisa bakwai na ’yan mat ana yin aure ne kafin su cika shekara 18.