Ma’aikatar Kula da Harkokin Aikin Hajji da Umarah ta kasar Saudiyya ta fitar da sharuddan da ta wajabta amfani da su yayin gudanar da aikin Hajjin bana.
Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da Saudiyya ta sanar da cewa a bana mutane daga kasashen waje, ko da ‘yan asalin Saudiyya ne, ba za su shigo kasar don aikin Hajjin ba a kokarin kasar na takaita yaduwar cutar coronavirus.
A cewar sanarwar, ba za a bar dattawa ‘yan shekara 65 da sauran mutane masu cututtuka masu tsanani su halarci gudanar da ibadar a bana ba.
- Mazauna Saudiyya ne kadai za su yi aikin Hajji a bana
- Saudiyya na duba yuwuwar dakatar da aikin hajjin bana
“Dole ne a yi wa maniyyata tsatstsauran gwaji kafin ma su samu izinin tafiya aikin kuma za a tabbatar da bayar da tazara yayin aikin”, inji sanarwar.
Kazalika, hukumar ta ce za a rika yi wa alhazai gwajin cutar a kullum, iya tsawon kwanakin aikin Hajjin.
Dole ne kuma a killace mahajjatan bayan kammala aikin Hajji don a tabbatar ba su kamu da cutar ba kuma su je yada wa wasu kasashensu.
Cutar coronavirus dai ta yi matukar illa ga harkokin ibada a kasar ta Saudiyya ta yadda sai da ta kai ga rufe masallatan Harami a biranen Makkah da Madinah.
Gwamnatin Saudiyya ta takaita halartar aikin Hajji a bana ne zuwa wadanda ke zaune a kasar a halin yanzu kadai, tana mai cewa mazauna wajen kasar ba za su halarci ibadar ba ta bana bana ba, kuma ta takaita adadin maniyyatan da za su yi aikin Hajjin da zai gudana a cikin wata mai zuwa ne domin kare yaduwar annobar coronavirus.
Ma’aikatar Kula da Harkokin Umarah da Aikin Hajji ta Saudiyya ta ce ‘yan ko’ina a sassan duniya za su iya yin aikin Hajji, amma da sharadin ta kasance yanzu haka suna cikin kasar.
“Takaitaccen adadin mutane ‘yan kowace kasa da ke zaune cikin Saudiyya a yanzu haka za su iya yin aikin Hajji”, inji sanarwar, amma ba ta ambaci adadin alhazan da aka kayyade za su halarci ibadar ba.
- Saudiyya: 3,379 sun kamu da COVID-19 a ranar dage dokar kulle
- Saudiyya na duba yiwuwar dakatar da aikin Hajjin bana
- Cutar Kurona: Allah Ya sa kada ta hana Aikin Hajji!
Hakan na nufin mazauna wasu kasashe, ciki har da ’yan asalin Saudiyya da ke kasashen ketare ba sa daga cikin wadanda za su yi babbar ibadar a wannan shekarar ke nan.
Sanarwar ta kara da cewa mahukuntan kasar sun dauki matakin ne saboda kare alhazai da sauran jama’a daga barazanar kamuwa da cutar coronavirus a lokacin aikin Hajji.
“An yanke hukuncin hakan ne domin tabbatar da ganin an yi Hajji cikin aminci tare da kare lafiyar al’umma yadda ya kamata ta hanyar bin matakan kariya sau da kafa, da kuma bayar da tazara yadda ya dace”, inji ma’aikatar.
Ta kara da cewa “an dauki matakin ne sakamakon yadda ake kara samun hadarin yaduwar cutar a wuraren da jama’a ke taruwa.”
Hajji shi ne aikin ibada da ya fi tara al’ummar Musulmi daga ko’ina a fadin duniya a wuri daya a lokaci guda. A shekarar da ta gabata, alhazai miliyan 2.5 ne suka gudanar da aikin Hajji a bara.