Gwamnatin Saudiyya ta yanke wa mutane 11 hukuncin dauri na shekara 65 da tarar Riyal miliyan 29 bayan kama su da laifin almubazzaranci da dukiyar baitul mali.
Majiya daga ofishin mai gabatar da kara na Saudiyya ce ta bayyana hakan a cewar wani rahoto da BBC ya wallafa.
Majiyar ta ce binciken da aka yi ya sa an kama mutum 11 da kuma wasu kamfanoni da laifin samar da gungun masu tafka laifi ta hanyar wadaka da kudin gwamnati.
Binciken ya nuna cewar, wadanda aka yanke wa hukuncin an same su ne da laifin sayen man dizel mai dinbin yawa.
Wannan dai yana da nasaba ne da yadda masu laifin suka mallaki gidajen sayar da mai, sannan suka sayar da shi ga wasu mutanen wadanda su kuma suka sayar da shi a kasashen waje.
Haka nan an kama su da laifin halasta kudin haram, da rufa-rufa, da zamba, da yin karan-tsaye ga tsarin sanya ido kan hada-hadar kudi.
Kotun ta kuma bayar da umurnin kwace na’urori da kadarorin da aka yi amfani da su wajen aikata laifukan da kuma abubuwan da suka samu.
Haka nan kuma za a kori ’yan kasar waje wadanda ke cikin wadanda aka yanke wa hukuncin bayan sun kammala shekarun da aka yanke masu.