kasar Saudiyya ta fadi a ranar Talatar da ta gabata cewa ta dakile wani yunkurin kai harin bam da kungiyar IS ta yi shirin kaiwa ga hedkwatar Ma’aikatar Tsaro ta kasar.
Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters, da ya rubuto labaran ya ce, Saudiyyar ta kuma kama mutane da dama da ake zargi da yin leken asiri a kasar ga wasu kasashen waje.
Wadanda suke yunkurin kai harin bam din sun hada da ’yan kasar Yemen biyu da suke zaune a Saudiyya wadanda aka tsare su tare da wadansu ’yan kasar Saudiyyar biyu da su ma ake zargi da hannu a shirin kai hari ga Riyadh fadar kasar kamar yadda bangaren tsaro na fadar Sarkin kasar.
Saudiyya ta yi fama da hare-haren bam da na harbin bindiga daga ’yan bindigar IS da suke kai hare-hare ga jami’an tsaro da kuma ’yan Shi’a.
Maharan suna samun horo ne kan yadda za su yi amfani da bam din da ake yin jigida da shi, inji majiyar tsaron, yayin da mahukuntan kasar suka ce sun kwato gurneti da dama da bindigogi a lokacin samamen da suka kai ga maboyar ’yan ta’addan.
A wani labarin kuma kafar labarai ta SPA ta ruwaito wata majiyar tsaro tana cewa, mahukunta sun bankado “ayyukan leken asiri don amfanin wasu kasashen waje” daga wani rukunin mutane da ba ta ambata ba.
Wata majiyar tsaro da ta ki bayyana sunanta saboda muhimmancin batun ya shaida wa Reuters cewa ana zargin mutanen ne da “yin leken asiri tare da alaka da wasu kungiyoyin kasashen waje ciki har da kungiyar Ikhwanul Muslimina ,” wadda mahukunta Saudiyya suka ayyana da kungiyar ’yan ta’adda.
“An zargi rukunin mutanen da yin hulda da karbo kudade da sauran tallafi daga wasu kasashe domin cutar da Saudiyyar ta hanyar wargaza harkokin tsaro a kokarin da suke yi na juyin mulki ga shugabannin Saudiyyar don amfanin Ikhwanul Muslimina,” inji majiyar.
Sai dai majiyar ta ki bayyana suna da kasashen da mambobin rukunin mutanen. Sai dai majiyar ta ce daya daga cikin wadanda ake tsare da su, mamba ne na sojin Houthi da ta kaddamar da yaki da dakarun hadin gwiwa da Saudiyya ke jagoranta don kare gwamnatin kasar Yemen a shekara biyu da rabi da suka gabata.