Daga yanzu kasar Saudiyya ba za ta kara tilasta wa gidajen abinci su bambance kofofin shigar maza da mata ba, a wani mataki na kawo sauyi a kan lamuran nishadi.
Ana ganin wannan wani bangare ne na sassauta dokokin hulda a tsakanin jinsin maza da mata a kasar domin kasar ta kara samun karbuwa a idanun duniya musamman kasashen Turai. Gwamnatin Saudiyya ta rubuta a Twitter cewa: “Daga yanzu ba dole ba ne rabe kofar shiga ta maza da kuma ta mata a gidajen cin abinci da sauran wuraren da jinsunan biyu ka iya haduwa.”
Tunda dadewa dama masu shaguna ko wuraren cin abinci na kasuwa a ka’ida sai sun samar da kofofin shiga na maza daban da na mata, ga duk wata iyalai da ta je wurin, don kauce wa haduwar maza da mata. A cikin wuraren akwai shamaki ko shinge na gilashi da ake sanyawa wanda ke hana haduwar maza da mata wuri guda koda kuwa tare suke ko iyalan gida daya ne.
Wannan tsari tun daga shekara daya ko biyu da suka gabata aka fara ganin sauyinsa, ta yadda wuraren sayar da abincin suka daina yin wannan shamaki. Ana ganin wannan mataki a matsayin karin wata hanya da kasar ta dauka daga irin sauye-sauyen da ta sanya a gaba, bayan irin sukar da ake mata kan murkushe ’yan hamayya inda babban misali na baya-bayan nan shi ne mummunar kisan gillar da aka yi wa dan jarida Jamal Kashoggi.