Ma’aikatar Harkokin Kasashen Wajen Saudiyya, ta bukaci a kawo karshen rikicin yankin Gaza da Gabashin birnin Kudus.
Saudiyya ta nuna goyon bayanta ga Falasdinawa, tare neman kawo karshen zubar da jinin da Isra’ila ke yi.
- ’Yan bindiga sun harbe dan Sarkin Kontagora
- An fara zaman sulhun El-Rufai da kungiyar kwadago
- ’Yan sanda sun cafke masu satar mutane a Filato
Ministan Harkokin Wajen Saudiyan, Yarima Faisal bin Farhan, ya ce kasarsa na goyon bayan Falasdinawa kan irin ta’addancin da ake musu.
A cewarsa, kasarsa na goyon bayan samar da halastacciyar kasar Isra’ila a kowane lokaci tare da Gabashin birnin Qudus a matsayin babban birninta, matsayar da kasar ke kai tun 1967.
Yarima Faisal, ya bayyana hare-haren sojin Isra’ilan kan yankin na Gaza a matsayin abin kunya wanda ke rura wutar ayyukan ta’addanci.
Ya bukaci kawo karshen hare-haren daga bangaren Isra’ila da kuma sojin Hamas da ke mayar da martani.