✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Saudiyya ta bai wa Kano da Abuja tallafin dabino albarkacin watan Ramadana

Cibiyar Bayar da Agaji da Jin Ƙai ta Sarki Salman (KSrelief) ce ta ɗauki nauyin bayar da tallafin da take yi duk shekara.

Gwamnatin Saudiyya ta bai wa babban birnin Nijeriya Abuja da kuma Jihar Kano tallafin tan 100 na dabino albarkacin watan Ramadana.

Ofishin Jakadancin Saudiyya ya gudanar da gagarumin bikin bayar da tallafin dabinon ne a wani ɓangare na ayyukan agaji da yake yi duk shekara.

Shirin wanda Cibiyar Bayar da Agaji da Jin Ƙai ta Sarki Salman (KSrelief) ta ɗauki nauyin gudanarwa, na da nufin tallafa wa iyalai masu ƙaramin ƙarfi a faɗin ƙasar da kuma ƙarfafa danƙon zumunci tsakanin ƙasashen biyu.

A yayin miƙa tallafin, Jakadan Saudiyya a Nijeriya, Faisal bin Ibrahim Al-Ghamdi, ya jaddada ƙwazon Masarautar Saudiyya kan ayyukan jin kai.

Ya kuma bayyana matuƙar godiyarsa ga Sarki Salman bin Abdulaziz Al Saud da Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman bin Abdulaziz Al Saud bisa goyon bayan da suke ba wa musulmi da al’ummomi masu rauni a duniya baki ɗaya.

Ya kuma jaddada cewa Saudiyya na nan daram a kan ƙudirin da ta ɗauka na samar da haɗin kan Musulunci da kuma bayar da agaji ga mabuƙata.

Ambasada Al-Ghamdi ya bayyana cewa rabon na bana ya haɗa da tan 50 na dabino na Abuja da kuma wani tan 50 na Kano, a ci gaba da al’adar Saudiyya ta taimaka wa Nijeriya ta hanyar bayar da agaji.

Ya bayyana hakan a matsayin wata babbar manufar Masarautar don ɗaukaka al’ummar Musulmi, rage raɗaɗi, da inganta haɗin kai, musamman a lokuta masu muhimmanci na addini kamar watan Ramadana.