Gwamnatin kasar Saudiyya ta ba wa Najeriya tallafin kayan asibiti na Dala miliyan daya domin yaki da cutar COVID-19.
Jakadan Saudiyya a Najeriya, Faisal Ebraheem Alghamdi, ya mika kayan ga Babban Sakatare Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya, Abdulazeez Mashi, a Abuja ranar Talata.
Kayan asibitin sun hada da na’uarar taimaka wa numfashi guda 23, da kuma tufafin aikin tiyata, safar hannu da takunkumin aikin tiyata da sauransu.
Da yake karbar kayan, Babban Sakataren na Ma’aikatar Lafiya, ya yi godiya tare da cewa za a raba kayan ga asibitoci a Najeriya.
Jakadan na Saudiyya ya ce, kasar ta bayar da tallafin ne da zimman karfafa kakkyawan dangantaka tsakaninta da Najeriya.
Alghamdi ya kara da cewa kasarsa ta shiyar gudanar da ayyukan kula da lafiya 12 sa yankunsa siyasa shida na Najeriya domin yakar cutar makanta, yanar ido da kuma ciwon zuciya.
Ya ce kawo yansu, kasarsa ta bayar da tallafin abinci na kusan Dala miliyan 10 ga ’yan gudun hijira a jihohin Borno, Yobe da Zamfara.