✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Saudiyya ta ba da tallafin Dala miliyan 10 ga ’yan gudun hijirar Ukraine

Saudiyya ce kasa ta uku a duniya da ta fi ba da tallafi ga mabukata.

Sarki Salman na Saudi Arabiyya ya bayar da tallafin Dala miliyan 10 ga ’yan kasar Ukraine sama da miliyan daya da suka tsere zuwa kasashe daban-daban sakamakon mamayar Rasha a kasarsu.

Ana gudanar da shirin ne tare da hadin gwiwa da gwamnatin kasar Poland da kuma Majalisar Dinkin Duniya.

Cibiyar Bayar da Agaji ta Sarki Salman, ta sanar cewa: “Sarki Salman ya umurci ‘KSrelief’ da ta ba da agajin gaggawa na magunguna da mafaka na Dala miliyan 10 ga ’yan gudun hijirar Ukraine a kasashe makwabta.”

Babban Mai Kula da cibiyar, Dokta Abdullah Al-Rabeeah, ya ce umarnin sarkin kari ne a bisa wanda Masarautar ke yi na taimaka wa mabukata da kuma rage radadin da suke ciki a duniya.

Ya jaddada kudurin kasar na taimaka wa ’yan gudun hijirar da suka tsere daga Ukraine zuwa Poland da sauran kasashe makwabta da cewa hakan na daga kudurin kasar na taimaka wa mutanen da ke cikin mawuyacin hali a fadin duniya.

Shugaban ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai a hedikwatar Ofishin Jakadancin Saudiyyar da ke Warsaw, babban birnin kasar Poland a ranar Litinin.

Hukumar bayar da agajin ta Saudiyya tana gudanar da ayyukan jinkai da suka zarta 2,000 a kasashe 85 a fadin duniya.

Ayyukan da suka hada da samar da abinci da kula da lafiya da bayar da ilimi da samar da ruwa da tsaftar muhalli da sauransu, in ji shugaban.

Saudi Arabiyya na daya daga cikin manyan kasashe masu ba da tallafi a duniya.

A bara, Masarautar ta kasance a matsayi na uku a duniya kuma ta daya a kasashen Larabawa wajen bayar da tallafi, inda ta bayar da tallafin da ya haura dala miliyan 841.

%d bloggers like this: