✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Saudiyya: Sarki Salman ya sa a kara wa’adin zaman baki kyauta

Saudiyya ta hana jirage shigowa kasar kai tsaye daga wasu kasashe 10.

Sarki Salman bin Abdulaziz na kasar Saudiyya ya ba da izinin tsawaita wa’adin zama a kasar da takardun biza ga baki masu shiga da wadanda ke kasar kyauta.

Sarki Salman ya ba da umarnin tsawaita wa’adin takardar zama a kasar, da bizar ziyara a karon farko da ta sake komawa kasar kyauta ne har zuwa ranar 30 ga watan Nuwamba mai kamawa.

Hakan na kunshe ne a shafin Masallatai Biyu Masu Alfarma, wadanda Sarkin ne Shugaban Majalisar Zartarwarsu.

Wannan sanarwa na zuwa ne kwanaki kadan bayan Saudiyya ta sanar da soke tsarin bayar da tazarar COVID-19 da sauransu a masallatan masu alfarma, tare da ci gaba da karbar masu zuwa Umrah yadda aka saba a baya.

Sai dai kuma ta ce har yanzu takunkumin da kasar ta sanya ga jirage masu shigowa kai tsaye daga wasu kasashe 10 tana nan tana aiki.

Kasashen su ne: Afghanistan, Masar, Pakistan, Indiya, Indonesiya, Turkiyya, Lebanon, Habasha, Vietnam da kuma Brazil.