Sarki Salman bin Abdulaziz na kasar Saudiyya ya ba da izinin tsawaita wa’adin zama a kasar da takardun biza ga baki masu shiga da wadanda ke kasar kyauta.
Sarki Salman ya ba da umarnin tsawaita wa’adin takardar zama a kasar, da bizar ziyara a karon farko da ta sake komawa kasar kyauta ne har zuwa ranar 30 ga watan Nuwamba mai kamawa.
- Lalata da dalibai: Poly Bauchi ta kori malamai daga aiki
- Ambaliya ta tilasta wa ango da amarya zuwa bikinsu a tukunyar girki
Hakan na kunshe ne a shafin Masallatai Biyu Masu Alfarma, wadanda Sarkin ne Shugaban Majalisar Zartarwarsu.
Wannan sanarwa na zuwa ne kwanaki kadan bayan Saudiyya ta sanar da soke tsarin bayar da tazarar COVID-19 da sauransu a masallatan masu alfarma, tare da ci gaba da karbar masu zuwa Umrah yadda aka saba a baya.
Sai dai kuma ta ce har yanzu takunkumin da kasar ta sanya ga jirage masu shigowa kai tsaye daga wasu kasashe 10 tana nan tana aiki.
Kasashen su ne: Afghanistan, Masar, Pakistan, Indiya, Indonesiya, Turkiyya, Lebanon, Habasha, Vietnam da kuma Brazil.