Ma’aikar ta ce ta tantance kimanin mutum dubu 440 da za ta ba fara yi wa rigakafin cutar a fadin kasar.
- Za a kula da lafiyar masu cutar AIDS kyauta a Kano
- Tsohon Ministan Ilimi Farfesa Agada ya rasu
- Rashin tsaro: Za mu hada kai da gwamnonin jam’iyyun adawa — Gwamnonin APC
A kwanakin baya Ma’aikatar Lafiyar Saudiyya ta sanar da cewa za ta samar da wadaccen rigakafin cutar wanda za a yi wa ’yan kasar kyauta.
Mataimakin Sakataren Ma’aikatar, Dokta Abdullah Al-Asiri ne ya sanar da hakan yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa a kowace rana kan annobar coronavirus a kasar.
Al-Asiri ya ce suna sa ran akalla kashi 70 cikin 100 na jama’ar Saudiyya za su amfana da rigakafin kyauta daga yanzu zuwa karshen shekarar 2021.
Ya bayyana cewa kasar na cikin kasashe ashirin na G20, masu karfin tattalin arziki a duniya da suka fara daukar matakan kariya da samar da rigakafin kyauta ga mutanen da suka kamu da cutar.