✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Saudiyya na jagorantar taron G20 kan inganta rayuwa bayan COVID-19

Kasar Saudiyya na karbar bakuncin shugannin kasashen duniya 20 masu ƙarfin tattalin arziki (G20) a babban taron kwana biyu da za ke gudana a kasar.…

Kasar Saudiyya na karbar bakuncin shugannin kasashen duniya 20 masu ƙarfin tattalin arziki (G20) a babban taron kwana biyu da za ke gudana a kasar.

Taron na karbar bakuncin shugabannin kasashen na G20 ne daga ranar Asabar 21 ga Nuwamba, 2020.

Sarki Salman Bin Abdulazeez na Saudiyya ne ke jagorantar taron da ya hada da shugabannin G20 da na manyan kungiyoyin duniya.

Za a kwashe kwana biyun ana tattaunawa kan abubuwan da suka faru a bana da kuma lalubo mafita ga kalubalen da duniya ke fuskanta a halin yanzu.

Taron da Sarki Salman ke matsayin mai masaukin baki shi ne mafi girma da aka taba yi da nufin samar wa duniya mafita daga halin da ta shiga.

Zai kuma mayar wa da hankali kan irin rawar da kasashen za su taka wurin karewa da kuma inganta rayuwar al’ummomi bayan gushewar annobar corinavirus.

Karon farko ke nan da Saudiyya ke jagorantar taron, mai karbar bakuncin kasashe mafiya karfin tattalin arziki na duniya.

Gwamnatin kasar ta ce ta samu wannan nasarar ce sakamakon shirinta na kawo sauye-sauye da bunkasa tattalin arzikin kasar, zuwa shekarar 2030.
%d bloggers like this: