Kasar Saudiyya ta yi tir da harin Kungiyar Boko Haram a jihar Borno, wanda ya sabbaba asarar rayukan mutane da dama da jikkata wasu da ba su ji ba, ba su gani ba.
Ma’aikatr Harkokin Wajen Saudiyya ta ce: “Muna Allah-wadai da harin ta’addancin da a ka kai a Arewa maso Gabashin Najeriya wanda ya salwantar da rayukan mutane da dama ya kuma jikkata wasu da ba su ji ba, ba su gani ba”.
- Boko Haram ta kone garin Kareto, ta kashe mutm 13 a Damboa
- Kisan Manoma: Dabararka ta gaza —Majalisa ga Buhari
- Zabarmari: Manoman da aka kashe ba su nemi izini ba —Garba Shehu
“Muna ta’aziyya ga iyalan wadanda abun ya ritsa da su da Gwamnatin Najeriya, da fatan Allah Ya ba wadanda suka ji rauni lafiya.
“Saudiyya na goyon bayan gwamnatin Najeriya a yaki da ’yan ta’adda da kuma kare lafiyar jama’a”, inji sakon.
Ita ma kasar Bahrain ta yi Allah-wadai da harin a cikin sakon jajenta ga iyalan wadanda abun ya ritsa da su, gwamnatin Najeriya da ma ’yan Najeriya, tare da addu’ar Allah Ya ba wadanda suka ji rauni lafiya.
Bahrain ta yi kira da a samar da wani hadin guiwa da zai hada kasashen duniya kan yaki da ayyukan ta’addanci.
A nasa bangaren, Babban Sakatare a Kungiyar Kasashen Musulmi ta OIC, Ibrahim Taha, ya jajanta tare da yin ta’aziyya ga iyalan wadanda abun ya ritsa da su da gwamnatin Najeriya da fatan Allah Ya ba wadanda suka jikkata lafiya.
OIC ta bayyana goyon bayanta ga gwamnatin Najeriya kan yaki da ta’addanci da kare lafiyar mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba.
Ita ma Kasar Amurka, ta yi ta’aziyya ga iyalan da ’yan uwa da abokan arzikin wandanda aka kashe da wadanda aka yi garkuwa da su.
Amurka ta jaddada goyan bayanta ga gwamnatin Najeriya kan yaki da ’yan ta’adda da kare lafiyar al’umma.